Ikon Tarurrukan Addu’a

24/09/2026

Menene Bautar Allah Ɗaya?

01/10/2026

Ikon Tarurrukan Addu’a

24/09/2026

Menene Bautar Allah Ɗaya?

01/10/2026

Yadda za mu bi Hanyar Tsarki ba tare da Mayar da Addininmu bin Dokoki Kawai Ba

A cikin littafin The Whole Christ, Dr. Ferguson ya ba da bayani mai kyau game da ma’anar bin dokar Allah: “Rike dokar Allah kawai ba tare da fahimtar Allah da kansa a matsayin Uba mai kauna da jinkai ba.” Idan muka raba dokar Allah da bukatunta daga Allah mai kauna da karimci wanda dokar tasa ce, tabbas za mu ga cewa kokarinmu na bin tsarki yana karkata zuwa hanyar shari’anci mara amfani. Don haka, dole ne a kowane lokaci mu bi tsarki ta hanyar tunawa da wane ne Allah da kuma dalilin da ya sa yake kiranmu mu zama masu tsarki.

A cikin 2 Korinthiyawa 1:3–4, Bulus ya yaba wa Allah kuma ya ba mu siffa mai ban al’ajabi game da ko wane ne shi: “Godiya ga Allah da Uba na Ubangijinmu Yesu Kristi, Uban jin ƙai da Allahn dukan ta’aziya, wanda yake ta’azantar da mu a cikin dukan ƙuncinmu.” Uban jin ƙai ya ta’azantar da mu a cikin ƙuncinmu ta wajen aiko da Ɗansa zuwa duniya don ya ceci masu zunubi. Saboda ƙaunarsa mai girma, Uban ya aiko da Yesu Kristi don ya fanshe mu daga rashin tsarki wanda muka jefa kanmu a ciki ta zunubinmu. Ubanmu ya aiko mana da Mai Ceto, Ubangiji Yesu Kristi, don ya mai da mu masu adalci a gabansa. Ta alheri kaɗai, ta wurin ba da gaskiya kaɗai, bisa dalilin aikin ceton Kristi kaɗai, muna da salama da Allah (Rom. 5:1–2).

Amma Ubanmu mai jin ƙai bai gamsu kawai ya baratar da mu kuma ya sa mu zama daidai a gabansa ba. Har ila yau, yana son mu zama masu tsarki kamar yadda Shi mai tsarki ne (1 Bitrus 1:15–16). Saboda haka, Allah kuma yana aiki don ya sabunta mu bisa ga surar Ubangijinmu Yesu Kristi. Don haka, bisharar nan ita ce

Kristi, bayan ya fanshe mu da jininsa,
kuma yana sabunta mu ta wurin Ruhunsa zuwa kamaninsa. (Koyarwar Heidelberg 86)

Saboda haka, an kira mu mu bi tsarki cikin tabbataccen sani mai ta’aziyya cewa tsarki shi ne nufin Ubanmu a gare mu, kuma Kristi, ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki, yana aiki don cika wannan nufi. An kira mu mu shiga kuma mu ba da haɗin kai ga wannan aiki; duk da haka, nasarar aikin sabuntawa na Allah ba ta dogara a kanmu ba, sai dai a kan Allah, Uba, Da, da Ruhu Mai Tsarki, (or, Allah, uku cikin daya) wanda wannan aikin nasa ne. Ruhu Mai Tsarki yana tabbatar mana da wannan gaskiya a cikin 1 Tasalonikawa 5:23–24: “Allah na salama da kansa ya tsarkake ku sarai, bari dukan ruhunku da ranku da jikinku kuma su kasance marasa aibu a ranar zuwan Ubangijinmu Yesu Kristi. Shi wanda yake kiran ku mai aminci ne; tabbas zai aikata shi.” Allah yana son mu zama masu tsarki, saboda haka ya yi alkawarin yin aiki domin muradinsa ya cika a cikinmu.

Allah ya damu ƙwarai da tsarkakewarmu da sabuntawarmu domin yana son mu zama waɗanda suka dace da rayuwa tare da shi a mulkinsa. Mun sani cewa mulkin Allah al’amari ne na “adalci da salama da farin ciki” (Rom. 14:17). Allah ya sani cewa in babu adalci, mutanensa ba za su iya dandana salama da farin cikin mulkinsa ba. Ka tuna abin da ya faru sa’ad da ɗan-adam ya fāɗi: mun juya daga adalci zuwa rashin adalci. Ta yin haka, mun ɓata salama da muke morewa tare da Allah, maimakon haka muka haifar da gaba da shi. Mun canji farin cikin zumunci da shi da baƙin cikin nisanta da shi. Amma Allah mai ba da rai ne, wanda ya halicce mu domin mu rayu tare da shi cikin adalci, salama, da farin ciki. Saboda haka, ya yi niyyar maido da wannan dangantaka da mu (Far. 3:15).

Ubanmu na Sama mai jin ƙai yana son mu kasance kamar mutumin Zabura 1, wanda yake jin daɗin shari’ar Ubangiji kuma yana bimbini a kanta dare da rana. Me ya sa? Domin wannan mutumin

yake kamar itace
wanda aka dasa a gefen raƙuman ruwa
wanda yake ba da ’ya’yansa a kan lokacinsa,
kuma ganyensa ba ya bushewa.
A cikin duk abin da yake yi, yana samun nasara. (Zab. 1:3)

Muna jin daɗin shari’ar Allah sa’ad da muka fahimci cewa ita ce shari’ar nan mai albarkacin rayuwa ta Allahnmu mai ba da rai. Allah yana son mu bi tsarki domin yana son mu zama kafaffu, masu ba da ‘ya’ya, masu jimiri, da masu albarka a yanzu da kuma har abada. Nufin Uba a gare mu shi ne:

Farinciki da dukan zuciya a cikin Allah ta wurin Almasihu
da kuma ƙauna da murna na yin rayuwa
bisa ga nufin Allah
ta wajen yin kowane irin kyakkyawan aiki. (Koyarwar Heidelberg 90)

A cikin bin tafarkinmu na tsarkaka, godiya ga Almasihu ita ce babban maganin bin dokoki don samun kuɓuta. Ba ma bin tsarkaka domin mu sa kanmu mu zama karɓaɓɓu ga Allah ba. Muna bin tsarkaka ne cikin godiya ga fansa wadda take tamu ta wurin jinin Almasihu da kuma sabuntawa wadda Ruhun Almasihu yake tabbatarwa a cikinmu. Muna bin tsarkaka da farin ciki domin shi ne dalilin da ya sa aka halicce mu, aka kuma sāke halittarmu:

Domin ta wurin alheri aka cece ku ta wurin bangaskiya. Kuma wannan ba daga gare ku ba ne; kyautar Allah ce, ba sakamakon ayyuka ba, domin kada kowa ya yi fahariya. Domin mu ne aikinsa, waɗanda aka halitta cikin Kristi Yesu don kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya shirya tun da wuri, domin mu yi tafiya a cikinsu. (Afis. 2:8–10).

Allah ya tsare mu daga shari’anci kuma ya yi mana jagora da alherinsa da Ruhunsa yayin da muke bin tsarki.


An fara wallafa wannan talifi ne a shafin Blog na Ministirin Ligonier. [Blog ɗin Ministirin Ligonier]

William C. Godfrey

William C. Godfrey

Rev. William C. Godfrey fasto ne na Christ United Reformed Ikilisiya a Santee, Calif.