Yesu ne Sabuwar Haikalin

24/11/2026

Yesu ne Sabuwar Haikalin

24/11/2026

Mutane iri Shida da suke Sauraon Kalmar Allah

A cikin duniyar da ta cika makil da bayanai, akwai muryoyi da dama da suna neman hankalinmu. Duk da haka, a tsakiyar wannan hayaniyar, babu wasu kalmomi da suka kai Maganar Allah mahimmanci—abin da mai zabura ya kira “mafi zaƙi fiye da zuma” (Zab. 119:103). Bisa ga wannan, Yaƙub 1:22–25 ya gabatar da wata muhimmiyar tambaya: Ta yaya muke mayar da martani ga Maganar Allah? Shin muna saurara kawai ne, ko kuwa muna amfani da ita a cikin rayuwarmu?

Yaƙub ya ba da umarni, “Ku zama masu aikata maganar, ba masu ji kawai ba, kuna yaudarar kanku” (Yaƙub 1:22). Ba wai yana rage muhimmancin buƙatar ji ba ne; a maimako haka, yana karfafa masu karatu su kasance “masu hanzarin ji” (Yaƙub 1:19). Duk da haka, Yaƙub ya bayayana babban hadarin yaudarar kai na mutane da suke tunanin cewa sauraron Maganar Allah kawai shi ne asalin ibada ta gaskiya. Bangaskiya ta kwarai, in ji shi, tana bayyana ae ta ayukanmu, wato yadda muke rayuwa bisa gaskiyar da muka ji (Yaƙub 2:14–17).

Yaƙub ya kwatanta mai sauraro kawai da mutumin da, bayan ya lura da aibobinsa a madubi, ya tafi kuma ya manta abin da ya gani (Yaƙub 1:23–24). Wannan misali ya kwatanta babban wauta na jin Maganar Allah ba tare da yin amfani da ita ba. Madubin, a wannan yanayin, shi ne Maganar Allah kanta. Yana bayyana zunubinmu, ya bayyana ainihin yanayinmu na ruhaniya, kuma ya karkatar da mu zuwa ga Kristi—Shi kaɗai ne mai ikon gafarta mana kuma ya tsarkake mu daga dukan zunubi. Sauraron Maganar amma kuma a yi banza da kiran da take yi na tuba da bangaskiya shi ne watsi da alherin da take bayarwa da kuma wanzuwa a cikin zunubi ba tare da canji ba.

Gargadin Yaƙub yana kiranmu ne mu bincika kanmu. Wane irin masu sauraro ne mu? Ga ire-iren masu sauraro guda shida waɗanda suke wakiltar martani daban-daban ga Maganar Allah:

1. Malam Makaho

    Wannan mai ji yana duban madubi amma ba zai iya gani sarai ba saboda makantar ruhaniya. Ko da yake yana iya karantawa ko nazarin Nassin Littafi Mai Tsarki, ya gaza gane zunubi yadda Allah ya bayyana shi. Yana kiran mugunta nagarta, nagarta kuma mugunta (Ish. 5:20). Rayuwarsa tana cike da dabi’un zunubi, duk da haka bai damu da hanyoyin zunubi da suka mamaye rayuwarsa ba. Abin da yake bukata shi ne aikin sabuntawa na Ruhu Mai Tsarki domin ya buɗe idanunsa ga gaskiya.

    2. Uwargida Mai Tsoro

      Ta san cewa tana da aibu, amma tana tsoron fuskantar su. Kamar wanda yake guje wa likita don tsoron ganewar cuta mai muni, Malama Mai-Tsoro tana kin amincewa da abin da Kalmar Allah ta nuna mata game da zunubinta. Duk da haka, ’yanci na gaskiya ba ya zuwa ta hanyar kaucewa, sai dai ta hanyar kawo zunubinmu cikin haske da kuma juyawa ga Kristi cikin tuba da kuma ta wurin bangaskiya.

      3. Malam Mai- Ganin Kansa Mai Adalci

        Yana ganin kurakuransa amma yana ba da hujjar kansu. Da yake yana ganin kansa mutumin kirki ne, baya son ya karbi gyarra karɓar gyara. Sa’ad da aka fuskance shi, sai ya kauce wa alhakin, yana cewa, “Ba ni bukatar in canza—wasu ne ya kamata su canza.” Dogara da adalcin kansa ya makantar da shi ga bukatarsa mai zurfi na jin ƙai. Yana kama da Bafarisi a cikin misalin Yesu wanda ya yi addu’a, “Ya Allah, na gode maka, da yake ni ba kamar sauran mutane nake ba, mazambata, marasa adalci, mazinanta, ko ma kamar mai karbar harajin nan. Duk mako ina azumi sau biyu. Kome na samu nakan fitar da zakka” (Luka 18:11-12). Ko da yake ya bayyana kamar mai ibada ne, zuciyarsa tana da girman kai kuma ba ta tuba ba. Yesu ya tunatar da mu cewa bai zo don ya kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi zuwa ga tuba (Luka 5:32).

        4. Malama Mai Gani Komai Ba Zai Yi Kyau Ba

          Tana kallon madubi, ta yarda da aibobinta, amma ta gaskata cewa sun fi ƙarfin a tsarkake su. Maimakon ta juya ga Allah don samun jin ƙai, sai ta tsaya a kan baƙin cikinta da fid da zuciya, tana cewa, “Zunubina ya yi yawa da ba za a gafarta mini ba.” Abin da Malama Mai Ganin Komai Ba za yi Kyau \ba take buƙata shi ne begen bishara. Kamar yadda Robert Murray M’Cheyne ya faɗa cikin hikima, “Domin kowane kallo ɗaya da za ka yi wa kanka, ka yi kallo goma ga Kristi.” A cikin Kristi, akwai cikakkiyar gafara ga mai zunubi mafi muni wanda ya tuba ya kuma ba da gaskiya.

          5. Malam Mai Yin Biyayya Rabi-Rabi

            Kamar Sarki Saul a cikin 1 Sama’ila 15, shi ma yana yin biyayya ta zaɓi-zaɓi. An umarci Saul ya hallaka Amalekawa gaba ɗaya, duk da haka ya bar mafi kyawun dabbobi da kuma Sarki Agag. Ya kāre kansa ta hanyar nuna sadakar da ya yi. Amma annabi Sama’ila ya amsa da cewa, “Biyayya ta fi yin hadaya” (1 Sam. 15:22). Malam Mai-Rabi-da-Rabi yana yin wasu abubuwan da Allah ya faɗa, amma ba duka ba. Duk da haka, biyayya ta rabi da rabi har yanzu rashin biyayya ce. Mai sauraro na gaskiya yana miƙa kansa sarai ga Maganar Allah, ba wai kawai ga sassan da suka dace da shi ba.

            6. Malama Mai Hikima

              Wannan ita ce mai jin magana na gaskiya. Ganin aibobi da aka bayyana a cikin madubin Nassi, sai ta juya ga Allah cikin tuba kuma ta nemi tsarkakewa ta wurin Kristi. Kamar mai karɓar haraji a cikin misalin Yesu, tana addu’a, “Allah, ka yi mini jinƙai, ni mai zunubi!” (Luka 18:13). Yaƙub ya ce irin wannan mutumin “zai zama mai albarka a cikin abin da yake yi” (Yaƙub 1:25). Rayuwarta tana nuna alamun itacen da aka dasa a gefen koramu na ruwa a cikin Zabura 1—mai ba da ’ya’ya kuma mai jimiri.

              Yi La’akari da Kanka

              Don haka, wane irin mai sauraro ne kai? Ka tuna, albarkar Allah tana tabbata a kan waɗanda suke sauraro kuma suke yin biyayya. Ba domin biyayya tana samun ceto ba, amma domin tana kwarara ne daga zuciyar da alherin Allah ya canza ta da gaske. Kasancewa mai sauraron Maganar Allah, ashe, ba wai kawai sauraro da kyau ba ne ko kuma gaskata koyarwar Littafi Mai Tsarki a hankalce ba ne. Shi ne karɓar Maganar cikin tawali’u, da barinta ta bincike mu, kuma mu miƙa wuya gare ta cikin bangaskiya. Shi ne yin rayuwa tare da Ubangiji cikin hasken Maganarsa. Kamar yadda tsohuwar waƙar yabon nan take cewa:

              Ka dogara gare Shi, ka kuma yi biyayya, domin babu wata hanya dabam;
              Domin mu sami farin ciki cikin Yesu, sai ta wurin dogara gare Shi da kuma yin biyayya.


              An wallafa wannan makala ne da fari a Ministirin Ligonier Blog. [Blog ɗin Ministirin Ligonier]

              Brian Najapfour

              Brian Najapfour

              Dr. Brian G. Najapfour, fasto ne Ba’amurke ɗan asalin Filifin, wanda yake da digirin ThM daga Puritan Reformed Theological Seminary da kuma digirin PhD daga Theological University of Apeldoorn. Ya kasance mai hidimar bishara tun shekarar 2001, tare da ƙwarewar aikin fasto a duka ƙasashen Filifin da Amurka. Shi ne fasto na Ikilisiyar Heritage Reformed a Jordan, Ontario, inda yake zaune tare da matarsa, Sarah, da yaransu guda biyar. Shi ne marubucin littattafai da dama, ciki har da The Gospel-Driven Tongue da kuma A Hearer of God’s Word.