
An Haifi Maryamu Ba Tare da Zunubi Ba?
22/10/2026
Menene Ta’aziyyar Kirista a Lokacin Mutuwa?
29/10/2026Ta yaya Ikilisiya Za Ta Iya Kula da Membobinta Masu Nakasa?
A cikin ƴan makonni da aka kira ni a matsayin daraktan hidimar yara zuwa ikilisiyata ta yanzu, wani dattijo da matarsa suka nemi ganawa. Suka fara da wannan muhimmiyar tambaya: “Shin kana nan ne don ka yi hidima ga dukan yara a cikin ikilisiyarmu, ko kuwa mafi yawansu ne kawai?” Bayan na ba da amsar da ta dace (dukansu mana!), sai suka ci gaba da tambayata yadda na yi niyyar kula da yara biyar da iyalansu waɗanda nakasa ta shafa waɗanda mambobi ne na ikilisiyarmu. Waɗannan tambayoyi masu ƙalubale sun ratsa zuciyata kuma sun girgiza duniyar hidimata, suna kafa harsashin samun ci gaban hidimar nakasassu a cikin ikilisiyarmu.
Ana fara amsa tambayar yadda za a kula da mutane da iyalai da nakasa ta shafa a cikin ikilisiya ta hanyar fahimtar nauyin da ke kanmu na kula da dukan mambobin ikilisiya. Hidima ga masu nakasa ba na zaɓi ba ne, ko da kuwa babu mutane da yawa masu nakasa a cikin ikilisiyarku. Ba hidima ba ne da za mu mayar da hankali a kai bayan mun kammala hidimomi “mafi mahimmanci” ga yara, matasa, da sauran su. Kusan kowace ikilisiya ta gida tana da wani a tsakiyarta wanda nakasa ta shafa, ko a bayyane take ko kuma a ɓoye. Kuma akwai mutane da yawa a cikin al’umma waɗanda ke marmarin ikilisiya ta rungume su su ma.
A cikin 1 Korinthiyawa 12, Manzo Bulus ya kwatanta ikilisiya a matsayin jiki ɗaya na Almasihu wanda aka gina da membobi da yawa. Bayan ya bayyana yadda dukan membobi suke da bambanci kuma kowanne yana da muhimmanci, ya rubuta: “Gaɓoɓin jiki waɗanda suke ganin kamar sun fi rauni, su ne waɗanda ba za a iya rasa su ba . . . domin kada a sami rabuwa a jikin, amma membobin su kasance da kulawa ɗaya ga juna” (1 Kor. 12:22, 25). Yayin da muke amfani da waɗannan gaskiyar ga mutane masu buƙata ta musamman, an kira mu ba kawai mu kula da su yadda ya kamata ba, har ma mu gane cewa su mambobi ne da ba za a iya rasa su ba a jikin Almasihu.
An kwatanta ikilisiya a cikin Nassi ba kawai a matsayin jikin Almasihu ba, har ma a matsayin iyalin Allah. Saboda haka, yayin da aka kira mu mu kula da mutane masu buƙata ta musamman a matsayin sashen jikin, dole ne mu yi hakan da zuciya ta iyali. A matsayinmu na ’yan’uwa maza da mata a cikin Almasihu, muna da dangantaka ta iyali da kuma ƙaunar juna a cikin Almasihu. Tare da waɗannan siffofi guda biyu na ikilisiya a cikin zukatanmu, ga abubuwa guda biyar na zahiri game da yadda za mu kula da mutane da kuma iyalai da nakasa ta shafa:
Haɗa Kowa
A matsayin iyalin ikilisiya, ya kamata mu so a haɗa kowane mutum a cikin ayyuka da rayuwar ikklisiya. Nakasassu daban-daban suna sa ya zama ƙalubale a saka mutum a cikin harkoki kuma ya zama wani ɓangare mai gudanarwa na jiki. Dole ne mu duba kowane fannin hidima na ikilisiya, daga ibada zuwa almajirtarwa zuwa mishan, da sauransu, mu kuma tambayi yadda za mu tabbatar da haɗa dukan membobinmu. Dole ne mu yi duk abin da zai yiwu don bai wa nakasassu damar ba kawai a haɗa su ba, har ma su kasance ’yan gari na kwarai (Afis. 2:19).
Samun Hanyar Shiga
Ɗaya daga cikin hanyoyin da suka fi bayyana da muke kula da nakasassu ita ce ta hanyar sa gine-ginenmu su kasance masu sauƙin shiga. Ta yaya dukan mutane za su iya yin sujada tare kuma a almajirantar da su tare idan ba za mu iya haɗuwa tare ba? Mayar da dukan wurarenmu masu sauƙin shiga ko da yaushe abu ne mai muhimmanci. Amma kuma dole ne mu yi ƙoƙari mu sa dukan shirye-shiryen hidimarmu su kasance masu sauƙin shiga ga kowa ma. Ta yaya za mu kula da masu matsalar ji da gani, da waɗanda ke buƙatar wurare masu natsuwa, da kuma waɗanda ke da nakasar fahimta? Shin wasu mutane suna buƙatar abokin taimako don shiga Makarantar Lahadi, karatun Littafi Mai Tsarki, da sauran abubuwan hidima? A matsayin iyalan ikilisiya, ya kamata mu nemi ba wa dukan mambobi cikakkiyar damar shiga rayuwar iyali.
Raba Kyaututtuka
Dukan mambobin iyalin Allah an ba su kyaututtuka na ruhaniya don amfanin kowa (1 Kor. 12:7). Wannan ya haɗa da dukan Kiristoci masu buƙata ta musamman ma. Saboda haka, yayin da ya kamata mu yi hidima kuma mu kula da mutane masu buƙata ta musamman, ya kamata kuma mu almajirantar da su kuma mu shirya su don yin amfani da kyaututtukansu don ɗaukaka Allah da kuma yi wa sauran mutane hidima. Iyalin ikilisiya ba ta cika ba in babu kyaututtukan da mutane masu buƙata ta musamman suke da su da za su bayar.
Dangantaka ta Gaskiya
Duniya kan kasance tana raina ko kuma tana daukar masu nakasa ba a matsayin cikakkun mutane ba. Har ma Kiristoci a wasu lokuta suna iya ganin nakasar mutum ne kawai, ba su ga mutumin da kansa ba. Sa’ad da muka rungumi juna a matsayin iyali, muna neman dangantaka ta gaske da mutane na gaske. Dole ne mu wuce matsayin kawai “kula” da mutane masu nakasa, mu kula da su da gaske. Mu san tarihin rayuwarsu. Mu san su. Mu ƙaunace su.
Hutu ga Masu Kula
Hanya ta ƙarshe da ikilisiya za ta iya kula da mutanen da nakasa ta shafa ita ce ta kula da masu kula da su. Ba wa iyaye damar fita da dare ko sa’o’i kaɗan na hutu daga wahalhalun da ke tattare da aikin kulawa yana da muhimmanci ga kulawa ta dogon lokaci. Yawanci abu ne mai sauƙi ga yawancin mutane su sami hutu ga kansu daga damuwar wannan duniya. Iyalan da nakasa ta shafa suna buƙatar taimako daga dangin ikilisiyarsu domin samun hutu da farfaɗo da jikunansu da rayukansu.
Kammalawa
A cikin duniyarmu wadda sau da yawa ke tattare da keɓewa, rarrabuwa, da rigima, Kiristoci ma za su iya kasancewa a rarrabe da juna cikin sauƙi. Amma, a matsayin ikilisiya, ya kamata mu rayar da gaskiyarmu ta fuskoki biyu: mu ne jikin Kristi da aka haɗa da juna, kuma mu ne iyalin Allah da aka kira mu ƙaunaci kuma mu kula da juna. Kiran zuwa ga hidimar masu buƙata ta musamman shi ne kiran kula da dukan mutanen Allah.
An wallafa wannan makala ne da fari a Ministirin Ligonier Blog. [Blog ɗin Ministirin Ligonier]


