
Ta yaya Ikilisiya Za Ta Iya Kula da Membobinta Masu Nakasa?
27/10/2026
Me ya sa Halin Kirki Yana da Muhimmanci a Hidima?
03/11/2026Menene Ta’aziyyar Kirista a Lokacin Mutuwa?
Maganar Allah ta bayyana mutuwa a matsayin sakamako mai ban tsoro na tawayen mutum ga Allah. Tun ma kafin faɗuwar iyayenmu na farko cikin zunubi, Mahaliccinmu ya gargaɗi Adamu a sarai cewa sakamakon ketare dokarsa mai tsarki shi ne mutuwa: “Amma itacen sanin nagarta da mugunta, kada ka ci daga gare ta, gama a ranar da ka ci, lallai mutuwa za ka yi” (Far. 2:17). Wace irin mutuwa ce Adamu da Hauwa’u suka fuskanta bayan sun karya dokar Allah?
Nan da nan bayan ya sanar da hukunci a kan Adamu, Hauwa’u, da macijin yaudara—kuma ya la’anci dukan halitta saboda kuskuren Adamu na farko—Allah ya “kori mutumin” (Far. 3:24) daga lambun Adnin, domin kada ya ci daga itacen rai “ya rayu har abada” (Far. 3:22). Da yake Adamu da Hauwa’u halittun Allah ne, Allh ya yanke musu hukuncin mutuwar jiki. Nan take aka fara aiwatar da wannan hukunci ta hanyar raba su da kasancewar Mahaliccinsu mai ba da rai. Wannan rabuwa, kamar kowace irin rabuwa da ba da dace ba, ta kasance mai matukar radadi.
Mutuwa tana da daci, kuma wannan dacin ya samo asali ne daga rabuwa da Aallah saboda zunubi. Amma akwai ta’aziya a cikin bishara. Labari mai daɗi na ceto shi ne cewa Allah wanda ya zartar da shari’a kuma ya la’anci ƙasa ya kuma samar da magani a cikin Kristi, makaɗaicin Ɗansa, zuriyar macen da aka yi alkawarinta wanda za ta murƙushe kan mai yaudarar nan mai kisa (Far. 3:15). Kamar yadda Manzo Bulus ya rubuta: “Dacin mutuwa zunubi ne, ikon zunubi kuma shari’a ce. Amma godiya ga Allah, wanda ya ba mu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Kristi” (1 Kor. 15:56–57). Kristi shi ne Babban Mai Sulhuntawa tsakanin Allah da mutum (Kol. 1:20–22) kuma babban Mai Nasara a kan zunubi da mutuwa.
Akwai babbar ta’aziya da ake iya samu har ma a lokacin mutuwa, amma ba ta taɓa kasancewa ba idan ba tare da Kristi ba. Littafi Mai Tsarki ya nuna fannoni guda uku cikin ƙarfi game da ta’aziyyar da ke akwai ga Kiristoci yayin da muke yin tunani a kan mutuwa, musamman sa’ad da mutuwa ta kusanto.
1. Kristi ne mai iko a kan mutuwa.
Na farko, Kristi shi ne mafi ɗaukaka bisa mutuwa. Ishaya ya kwatanta mutuwa a matsayin wani mayafi na duhu mai shake numfashi da ya mamaye dukan ’yan adam, yana yin annabci,
Kuma zai haɗiye a kan wannan dutse
bargo da aka shimfiɗa a kan dukkan al’ummai,
labulen da aka shimfiɗa a kan dukan al’ummai. (Isha. 25:7)
Amma Kristi ya fi girma:
Zai haɗiye mutuwa har abada;
kuma Ubangiji Allah zai share hawaye daga dukan fuskoki,
kuma zai kawar da zargin mutanensa daga dukan duniya;
gama Ubangiji ya faɗa. (Isha. 25:8)
Wannan tabbatacciyar magana ce da shela daga Allah: Ba wai kawai zai kawar da ikon mutuwa ba ne, amma zai haɗiye mutuwa kanta har abada, wanda wannan ya kai mu ga matsayi na biyu.
2. Kristi ya kawo karshen rabuwa da Allah da zunubi ya jawo wa yan Adam.
Na biyu, Kristi ya kawar da zargin mutanensa ta hanyar zubar da jininsa a matsayin hadaya a kan gicciye. Littafin Ibraniyawa ya rubuta,
Kuma kamar yadda aka ƙaddara wa mutum ya mutu sau ɗaya, bayan wannan kuma shari’a, haka Kristi ma, bayan an miƙa shi sau ɗaya domin ya ɗauki zunuban mutane da yawa, zai bayyana a karo na biyu, ba domin ya magance zunubi ba, amma domin ya ceci waɗanda suke zama cikin ɗokin jiransa. (Ibr. 9:27–28)
Kristi ya warware gagarumar matsalar barewa da ’yan Adam suka yi. Bugu da ƙari, Almasihu bai gamsar da fushin Allah mai adalci kawai ba, kuma bai wanke zunubanmu da jininsa kawai ba, har ma ya famshe mu daga la’anar Sharia ta wurin zama abin la’ana sabodamu a kan giciye. (Gal. 3:13). Ya saye mu da jininsa kuma ya biya hukuncin zunubinmu domin ya gabatar da mu ga Allah a matsayin taskarsa mai daraja kuma abin tamani. Mu ba na kanmu ba ne, kuma tabbas ba ma ƙarƙashin ikon mutuwa ba ne. Mu na Allah ne cikin Kristi.
3. Muna da tsaro a cikin Kristi.
Na uku, ta wurin ikon Allah an fitar da mu daga mulkin duhu (da mutuwa) kuma an kawo mu cikin haskensa mai ban al’ajabi (da rai): “Shi ne ya cece mu daga ikon duhu, ya kuma mayar da mu zuwa mulkin Ƙaunataccen Ɗansa, wanda a cikinsa muke da fansa, wato gafarar zunubai” (Kol. 1:13–14). Kuma babu abin da—ko da mutuwa ta zahiri ce—zai iya ƙwace mu daga hannunsa. Yesu ya ce:
Tumakina suna jin muryata, kuma na san su, suna kuma bina. Ina ba su rai madawwami, kuma ba za su taɓa halaka ba, babu kuma wanda zai ƙwace su daga hannuna. Ubana, wanda ya ba ni su, ya fi kowa girma, babu kuma wanda yake da ikon ƙwace su daga hannun Uban. (Yohanna 10:26–29)
A cikin rayuwa har ma ta wurin mutuwa, muna amintattu a cikin Kristi.
Kammalawa
Akwai abubuwa da yawa da ba mu fahimta game da mutuwa, kuma irin wannan tunanin da ba mu da cikakken bayani a kansa game da abin da za mu fuskanta sa’ad da lokacin mutuwa ya zo, na iya sa mu cikin rashin kwanciyar hankali. Wani marubuci ya nuna zurfin tunani: “Babban asirin nan na mutuwa, yadda yake cinye ƙananan asirai na rayuwa waɗanda ke cike da ruɗani! Mai karatu, a cikin wannan ƙaƙƙarfan sa’a za mu taɓa su duka; babban wahayi kuma zai biyo baya, a cikin hasken Al’arshi.”1 Amma ga Kirista, alkawarin ta’aziyya shi ne cewa abin da ke jiranmu bayan mutuwa shi ne madawwamin farin ciki a gaban Allah mai ba da rai, wanda a “hannunsa na dama akwai ni’ima har abada” (Zab. 16:11).
- B.M. Palmer, The Broken Home; ko kuma Darussa a cikin Bakin Ciki (New Orleans: E.S. Upton, 1890), 13–14. ↩
An wallafa wannan makala ne da fari a Ministirin Ligonier Blog. [Blog ɗin Ministirin Ligonier]


