Me Ake Nufi Da A Sake Haifar Mutum?

Yaya mutum zai iya kasancewa an sake haifarsa?

Sa'ad da Yesu ya gaya wa shugaban Yahudawa Nikodimu cewa, “Dole ne a sake haifuwarka,” Nikodimu ya tambaya cikin mamaki, “Yaya waɗannan abubuwa za su iya kasancewa?” Kimanin shekaru dubu biyu bayan haka, har yanzu mutane suna rikice game da kalmar nan “sake haifuwa,” ko da yake mutane da yawa fiye da kowane lokaci suna da'awar cewa sun sami wannan gogewa.

A cikin wannan ɗan littafin, Dokta R. C. Sproul ya warware rikicewar kuma ya bayyana dalla-dalla ma'anar kasancewa wanda aka sake haifa. Dokta Sproul ya tabbatar da cewa sabuwar haifuwa tana da mahimmanci ga ceto kuma ya ci gaba da nuna cewa wannan sake haifuwa madaukakin aikin Allah ne a cikin zukatanmu.

Jerin ɗan littafin Muhimman Tambayoyi na Dokta R. C. Sproul yana ba da taƙaitattun amsoshi ga muhimman tambayoyi waɗanda Kiristoci da masu bincike masu zurfin tunani suke yawan yi.

Ministirin Ligonier

Ministirin Ligonier

Mu ne zumuntar koyarwa ta Dr. R.C. Sproul. Mun wanzu don yin shelar, koyarwa, da kuma kāre tsarkin Allah cikin dukan cikarsa ga mutane da yawa gwargwadon iko. Manufarmu, sha'awarmu, da dalilinmu shi ne taimaka wa mutane su yi girma cikin sanin Allah da tsarkinsa.