Mene ne Muke Nufi Sa’adda Muke Magana Kan “Darajar Ran Ɗan Adam”
28/11/2025
Muhimmin Dalili da Ya Haifar da Barata
02/12/2025
Mene ne Muke Nufi Sa’adda Muke Magana Kan “Darajar Ran Ɗan Adam”
28/11/2025
Muhimmin Dalili da Ya Haifar da Barata
02/12/2025

‘Yancin Zaɓi: Me Wannan Ke Nufi?

Mene ne abin da matsayi na ‘Yancin-Zaɓi ya ƙunsa? Idan mace ta ce ita kan ta, ba za ta zubar da ciki ba, amma kuma ba ta hana wadda ke son zubarwa damar ta yi hakan ba, to wane dalili ne har zai iya hana irin wannan macen ita kanta ta zubar da ciki? Mai yiwuwa domin tana so ta haifi ‘ya’ya dayawa ne, yadda har ba ta ma tunanin ko akwai yanayin da za ta sami cikin da ba za ta so ba. Mai yiwuwa wannan macen tana tunanin cewa ɗan-tayi cikakken mutum ne mai rai, ko kuma ba ta tabbata ko wanne ne matsayin ɗan-tayi ba. Wataƙila ta gaskanta cewa ɗan-tayi mutum ne cikakke amma ba ta so ta tilasta wannan ra’ayi a kan wasu mutane. A nan mun ga ainihin abin da ke ƙunshi cikin matsayi na ‘yancin zaɓi. Shin ko zahiri ‘yancin zaɓi abu ne da ya dace? Ko muna da ɗabi’a na yin rayuwar nagarta, har ya kai ga za mu iya zaɓen abin da ba rayuwar nagarta ba ne? Wannan tambayar tana ɗauke da amsar ta a cikin ta.

Haka kuma, duk wata doka da aka kafa takan zo da sa iyaka, ko kuma tana ƙayyade irin damar zaɓi da mutum zai iya kasancewa da shi. Wannan shi ne ainihin tsarin doka. Idan ba ma so mu ƙayyade damar zaɓi da waɗansu ke da shi ta hanyar kafa dokoki, to sai dai mu daina kafa dokokin, sannan kuma mu daina kaƙa ƙuri’a. Ina tunanin cewa mutane dayawa za su yarda cewa ‘yancin zaɓi  dai a gaskiya ba cikakken ‘yanci bane. Babu wani ɗan Adam da ke da iko na cikakkiyar doka ga kansa da kansa. Idan dai ba wai mun yi shirin mu rungumi tsarin ɗabi’ar rayuwa na kowa-ya- yi abinda-ya dace-masa, irin wadda babu tabbaci na kiyaye doka da kuma al’umma kanta, to, dole ne mu tsere kamar hurawar iska, daga ra’ayin nan mai cewa mutum shi da kansa ke da hakkin kome bisa kansa. Idan muka fita daga yanayi na tunani kawai, zuwa abin da ido ke gani, sai in ce ko masu gwagwarmayar kare ‘yancin haƙƙin  zaɓi, za su nuna na-ƙi ga dokokin da suka tanada haƙƙi na tsare dukiyar su? Ko kuma, ɓarawo da ke shiga gidan wani ya sata masa talabijin yana da cikakkiyar haƙƙi na kan sa da kansa kai tsaye ya yi wannan zaɓi? Shin ko namiji yana da damar haƙƙin yi wa mace fyaɗe? Waɗannan tsauraran misalai suna nuna cewa, kada a ɗauki haƙƙi na‘yanci zaɓi a matsayin cikakkiyar ‘yanci ga mutum ga kansa kaɗai ba.

A daidai wane mataki ne ya kamata haƙƙi na ‘yanci zaɓi na mutum zai zo ƙarshe?  Ina ganin zai zo ƙarshe a daidai wurin da nawa haƙƙi na ‘yanci zaɓi ya taka haƙƙin na ‘yanci da rayuwar wani. Babu wani ɗa da ke cikin uwar sa, wanda ya taɓa kasancewa da haƙƙin ‘yancin zaɓa a hallaka ko kada a hallaka shi.  Ƙwarai kuwa, kamar yadda wasu ke faɗa, wuri mafi hatsari a ƙasar Amerika shi ne mutum ya kasance cikin mahaifar mace. Ga miliyoyin ‘ya’ya da ba a haifa ba, mahaifan ya zama kamar kurkuku ko ɗakin jiran mutuwa. A taƙaice ana kashe irin wannan fursuna ba tare da an saurari ƙarar sa, ko a ba shi damar faɗin maganar kare kansa/kanta ba. Wannan kisan ya haɗa da gutsuttsurawa gaɓa bayan gaɓa. Ko wannan bayani ya kasance mummunan hoto? Ko yana matuƙar damun tunani? A’a, amma zai iya zama haka ne har idan wannan bayani ba gaskiya ba ce.

Haƙƙi na ‘yanci zaɓi, duk da kasancewar sa abu tsattsarka, ba ya ɗauke da haƙƙin ‘yanci na son-rai, har ya kai ga hallaka ran mutum. Wannan ya zama ainihin yin ɓari da shari’a, kamar yadda ya kasance ɓari na jariri-mutum.

Wane abu ne a cikin haƙƙin‘yancin zaɓi ya sa shi ya zama da muhimmanci? Mene ne ya zuga Patrick Henry ga yin kukan cewa, “ Ku ba ni ‘yanci ko ku ba ni mutuwa”? Tabbas muna sha’awar yin naciya kan abin da muka ƙudira na kan mu da kanmu, kuma ra’ayin kasancewa cikin yanayin da wani daban zai so tilasta mana abu ne da muka tsana. Mu halitta ne da ke yin tunani, kuma muna darajanta ‘yancin da muke yin zaɓi. Yawancin mu za su tsani a sa su cikin kurkuku, amma ko a cikin kurkuku da ke da matuƙar tsaro mafi ƙarfi ma, ba dukan ‘yancin mutum na yin zaɓi ne ake iya kwacewa ba.

Wannan ƙa’ida ta nacewa kan abin da muka ƙudira da kanmu-wato, mu iya kasancewa da wani iko akan yanayin da muke ciki, da yadda rayuwar mu za ta kasance- ya kasance mummunan hana dama ne da aka yi wa kowane jariri da ba a haifa ba, wanda aka zubar da cikin. Ba ni da wata dama ko abin faɗa a kan zaɓin da uwa ta ta yi game da ko za ta zubar da ciki na,  ko kuma ta bari har sai na kai watanni taran nan. Rayuwa ta gaba ɗaya ta kasance a hannun ta. Da a ce ta yanke shawarar zubar da cikin, da an murƙushe rai na tun ma kafin a haife ni. Ni da kai mutane ne zahiri. Akwai lokacin da babu yadda muka iya yi game da tabbatar da morar muhimmin ‘yancin zaɓi na kan mu da kanmu. Akwai lokacin da gaba ɗaya mun dogara ne ga wani ko wata domin yin zaɓi da ya shafi na ainihin kasancewar mu a raye.

Wani muhimmin ɓangare kuma na wannan ‘yancin zaɓi shi ne tambaya ta, a wane lokaci ne ya dace a yi zaɓi nagari game da rai na ɗa/’ya da ke a ciki. (Domin wannan ya shafi kasancewa cikin tsarki dangane da batun jima’i, wanda kuwa ba batu ne da a ake yawan ambata ba in aka zo wannan zance.) Lokacin da ya dace a yi zaɓi na a haifi da/’ya ko kada a haifa, ba wai ana yin sa bayan an dauki ciki, har ɗan ya fara girma a cikin ba. Idan dai ba a yanayin fyaɗe bane, lallai,  yanayin jima’i ko da a yi amfani da kariya ko babu kariya dukan su matakai ne da suka shafi yin zaɓi.  Duk wani zaɓi da muke yi, ko ya danganci batun jima’i ko bai shafe shi ba, a kullum yana da sakamako. Kafaffen tsari ne na dabi’un rayuwa cewa kowa zai karɓi sakamakon irin zaɓi da ya/ta yi.

A lokacin da muka yi jima’i, mai yiwuwa ba mu yi niya ko kasance da sha’awar haifan wani mutum ba. Amma kuma mun sani cewa jima’i shi ne hanya na masomar haihuwar wani, kuma hakan na iya kawo haihuwar ɗa ko ‘ya. Kashe wannan ɗa ko ‘ya ba hanya mai dacewa ba ce, ba kuma tsarin kyakkyawar ɗabi’ar rayuwa bace domin magance abin da ya faru ba.

Daga Rubutu Kan Abortion (Zubar da Ciki) na R.C. Sproul.


An fara buga wannan tsararren rubutu ne a shafin ma’katar bishara ta Ligonier.

R.C. Sproul
R.C. Sproul
Dr. R. C. Sproul shi ne ya kafa Ministirin Ligonier, shi ne kuma mai bishara da koyarwa na farko a masujadar Saint Andrew’s da ke a Sanford, Fla., Shugaba na farko na Reformation Bible College, kuma Babban darekta na mujallar Tabletalk. Har yau, ana yaɗa shirin sa na Renewing The mind (sabonta tunani) a dubban tashoshin radiyo a kewayen duniya, haka kuma ana iya sauraro a yanar gizo. Ya wallafa litattafai fiye da dubu, sun haɗa da, The Holiness of God (TSarkin Allah), Chosen by God (zaɓin Allah), da kuma Everyone’s a Theologian (Kowa Dalibin Tauhidi ne). Ya zama sananne a kewayen duniya domin kalaman sa na kishin kare Littafi Mai Tsarki a matsayin babu kuskure a ciki, da kuma buƙatar mutanen Allah su tsaya daram bisa amincin su a kan Kalmar Sa (Allah).