Yaushe Yesu ya mutu?

27/08/2026

Mene Ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game Da Auren Mata Fiye Da Guda Ɗaya?

03/09/2026

Yaushe Yesu ya mutu?

27/08/2026

Mene Ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game Da Auren Mata Fiye Da Guda Ɗaya?

03/09/2026

Menene Kiristoci Suka Yi Imani Da Shi Game Da Wahayin Allah?

Allah yana sanar da kansa da kuma nufinsa ga ‘yan adam ne kawai ta hanyar bayyana kansa, wato wahayi. Wannan ya zama dole ga ‘yan adam a matsayin halittu domin su san Allah, domin Allah a matsayin Mahalicci ya daukaka kuma ya bambanta da halittunsa. ‘Yan adam ba za su iya sanin Allah ba sai dai idan ya zaɓi ya bayyana kansa. Ba za su iya samun saninsa ta hanyar hankalinsu, gogewa, ko ƙoƙarinsu ba in ba tare da bayyana kansa ba. Saboda haka, bayyanar da Allah yake yi wa kansa cikin alheri tana daidaita kanta da iyakacin fahimta da karfin dan Adam a matsayin halita. Ta wannan hanyar, duk ilimin da dan adam yake da shi – ko game da Allaj ko kuma game da nufinsa cikin halitta – yana zama ilimi irin na halitta, wanda yake kwaikwayon ilimin Allah na kansa a matsayin Mahalicci, da kuma iliminsa game da halittarsa.

Za mu iya bambance hanyoyi biyu da Allah yake sanar da kansa da kuma nufinsa ga ‘yan adam. Waɗannan hanyoyi biyu suna cika juna kuma suna aiki tare. Ana kiran na Wahayin da Allah ya bayyana ga kowa (wahayin gama-gari), inda Allah yake bayyana kansa ga dukkan mutane a ko’ina ta hanyar ayyukansa na halitta, kaddara, da kuma lamirin ɗan adam. Tsarin dabi’a da sararin samaniya suna nuna ikon Allah, hikimarsa, da yanayin allahntakarsa (Rom. 1:19–20). Gudanarwarsa na tarihi da al’amuran bil’adama suna nuna adalcinsa da alherinsa (Mat. 5:45; Ayyukan Manzanni 14:17). A cikin dabi’unsu na yau da kullum, ‘yan adam suna nuna sanin dabi’u da Allah ya dasa musu na sanin gaskiya da kuskure wanda yake nuna dokar dabi’a ta Allah (Rom. 2:14–15). Waɗannan duka ba kakkautawa, a sarari, bisa gaskiya, da iko suna bayyana ga ‘yan adam ko wane ne Allah a matsayin Mahaliccinsu da kuma abin da ya zama tilas su yi masa a matsayin halittun da aka yi da surarsa. Su shaidu ne madawwama kuma marasa yankewa, suna sanya ‘yan adam a kowane lokaci su zama masu alhakin bad da lissafi ga Allah.

Ko da yake wannan wahayi na kowa ya isa ya sanya dukkan ‘yan adam su zama masu alhakin ba da lissafi ga Allah, tushe ne kawai kuma bai isa ba domin ceton ‘yan adam. Furucin Bangaskiya na Westminster (1.1) ya bayyana shi haka:

Koda yake hasken da ke cikin halitta, tare da ayyukan Allah suna bayyana alheri, hikima, da ikon Allah har ta yadda mutane ba su da hujja; duk da haka ba su isa su bayar da wannan sanin na Allah ba, da kuma na nufinsa, wanda ya zama dole domin ceto.

Wannan ba don ‘yan adam suna da iyaka ba ne kuma saboda haka suna da gazawa a matsayinsu na halittu wajen fahimtar cikar bayyanar da Allah ya yi wa kansa. Allah koyaushe yana saukar da kansa yadda ya kamata a cikin bayyanar da kansa ga ‘yan adam. Maimakon haka, rashin wadatar ya samo asali ne daga gaskiyar zunubi da tasirinsa a kan hankali da nufin ‘yan adam. Kowane sashe na ɗan adam yadda aka yi shi da surar Allah an tsara shi ne don ya dogara ga kuma ya nuna kasancewar allahntakarsa da halinsa. Zunubi ya lalata hankali da dalilin ‘yan adam, yana kai su ga dannewa da karkatar da sanin Allah da suka samu ta hanyar wahayi na kowa. In ba tare da aikin Ruhu Mai Tsarki ba, mutane za su ci gaba da fahimtar abin da Allah ya bayyana a kuskure, ko kuma su ki karbar abin da aka bayyana a fili (sarari).

Wahayi na musamman ita ce hanya ta biyu da Allah yake sanar da kansa da nufinsa ga ‘yan adam, kuma duka biyun yana fassara ne da kuma ƙarawa a kan abin da yake bayyanawa a cikin wahayi na kowa. Yana bayyana ko wane ne Allah a matsayin Mai Fansa, manufofin ayyukansa na ceto a cikin tarihi, dangantakar alkawarinsa da mutanensa, da kuma babban shirin fansarsa ta wurin Yesu Kristi. An gudanar da wannan wahayi na musamman ta hanyoyi daban-daban a cikin tarihin fansa, ciki har da mafarkai, wahayi, bayyanar mala’iku, bayyanar a kamanin mutane (theophanies), da maganganun annabci. Duk da haka, ya kai kololuwarsa da cikarsa a cikin mutumtakar Yesu Kristi, wanda ta wurinsa Allah ya yi magana tabbatacciya (Ibi. 1:1–2) kuma wanda shi ne cikakken bayyanar Uba (Yohanna 1:18; 14:9). Babban nau’i na ƙarshe, kuma isasshe na wahayi na musamman, wanda shi ne na ƙarshe kuma isasshe, wanda kuma ke ba da shaida mai iko kuma marar kuskure ga duk wannan shi ne Littafi Mai Tsarki. Furucin Bangaskiya na Westminster (1.1) ya yi magana game da wannan kuma:

Ya faranta wa Ubangiji rai, a lokuta daban-daban, da kuma hanyoyi daban-daban, ya bayyana kansa, kuma ya sanar da nufinsa ga ikilisiyarsa; kuma bayan haka, domin kiyayewa da domin mafi kyawun kiyayewa da yaɗa gaskiya, da kuma tabbatarwa da ta’aziyyar ikilisiya a kan lalacewar jiki, da muguntar Shaiɗan da ta duniya, ya danka duka abin a rubuce; wanda ya sa Littafi Mai Tsarki ya zama mafi zama dole.

Wannan wahayi na musamman ne Ruhu Mai Tsarki yake sa shi ya yi tasiri domin ‘yan adam su sami wannan sanin Allah da yake da muhimmanci ga ceto, bangaskiya, da rayuwa ta ibada, kuma yana aiki tare da wahayi na kowa a matsayin dunkulalle guda don samar da Allah bayyana kansa ga ‘yan adam.


An fara wallafa wannan talifi ne a shafin Blog na Ministirin Ligonier. [Blog ɗin Ministirin Ligonier]

Matthew Dudreck

Matthew Dudreck

Dr. Matthew A. Dudreck mataimakin farfesa ne na Sabon Alkawari a Kwalejin Littafi Mai Tsarki ta Reformation a Sanford, Fla.