
Me Ya Sa Kuke Aiki?
15/12/2025
Ya Ya Kammannin Tuba Yake?
17/12/2025Ta Yaya Martin Luther Ya Mutu?
Martin Luther ya mutu a ranar 18 na Fabrairu, 1546. Wata ɗaya kafin wannan faruwa, ya rubuta wa abokin sa wasiƙa, yana nuna kukan sa game da fama na irin cututtuka da suka danganci irin shekarun sa, ya ce, “Ni, tsoho, gajiyayye, rago, marar ƙarfi, ga sanyi, ga hunturu, gaba da haka ma, mai ido ɗaya.” Sannan ya numfasa ya ce, “rabi matacce kamar ni, ƙila a bar ni cikin salama.”
Amma, ba a bar Luther cikin salama ba. An sami wani rikici a garin su na Eisleben. Saɓani yana yi wa zamantakewar su barazana, har kuma da tsarin rayuwar ikklisiya. Duk da kasancewar sa cikin rashin ƙarfi, sai Luther ya ɗauki niya ya je garin su don sasanta wannan rikici. Ya taso daga Wittenberg tare da ‘ya’yan sa maza guda uku, da kaɗan a cikin masu yi masa aiki. Sun kai har garin Halle. Ƙanƙara da tsananin ruwa mai isaka sun sa ƙetare rafuka ya zama da wahala. Sai Luther ya koma yana ba da sunaye ga manya-manyan ƙanƙara da ke gangarowa zuwa wurin da suke, yana kiran su abokan hamayyar ‘yan Anabaftis ne, da kuma su bishof na Papaproma na Roman Katolika. Duk da cewa ya kusa kai wa ga mutuwa, amma halin sa na ba da dariya na nan daram.
Halle shi ne garin Dr. Justus Jonas, wani tsohon abokin hidima na Luther. Tun lokacin mahawara da aka yi a Leipzig a shekara ta 1519, Jonas ya zama ɗaya daga cikin almajiran Luther na kurkusa. Jonas ya tsaya da shi a wurin Majalisar Worms. Ya jagoranci Gyaran ga samun ci-gaba a Wittenberg a lokacin da Luther ya tafi gudun hijira a Wartburg. Haka nan, yanzu Justus Jonas zai yi wa Luther rakiya a wannan tafiya tasa ta ƙarshe.
Luther da babban tawagar da yake tafiya da shi, sun yi gagarumin shiga cikin Eisleben. Wannan jarumin garin ya sami kyakyawan maraba, ga taron mutane suna shewa, suna raka shi da dawakai kamar basarake. Ya yi wa’azi a wannan lahadi, 13 na Janairu.
Amma tafiyar ta shige shi sosai. Luther ya rubuta wa matar sa Katie game da iska mai tsanani, da ruwan sama mai matuƙar sanyi, ban da ma zancen manya-manyan ƙanƙara masu hatsari. Luther yana tsananin rashin lafiya. Sai gobara da aka kasa shawo kanta ta kama, dab da ƙofar ɗakin Luther, tana barazana ga rayuwar Sa. Ginin da yake ciki ainihi ba ƙarfi gare shi ba. Simintin bangon ya yi ta faɗuwa wanda ya sa wasu duwatsu daga bangon suka fiffito. Wani dutse, da aka ce ya kusa girman filo, ya faɗo har ya kusan murƙushe kan Luther. Wannan mummunar faruwa ta sa Katie da ke can gida ta damu matuƙa. Ta rubuta wasiƙa cike da fargaba da damuwa. Don haka Luther ya sake rubuta mata, yana bayyana yadda yake kewan ta, ya ƙara da cewa, “Ina da mai kula da ni wanda ya fi ki, da dukan mala’iku, yana kwance a komin dabbobi, kuma uwatasa tana shayar da shi a mama, amma kuma Yana zaune a hannun dama na Allah, Uban, Mai-iko-duka.”
Luther ya rubuta wannan wasiƙa ranar 7 ga Febrairu. Kwanaki goma sha ɗaya bayan wannan ne ya mutu. Ya zama cewa garin Eisleben, wanda nan ne aka haife shi, yanzu an san shi a matsayin garin da ya mutu. ‘Ya’yan Luther maza su uku, su suka yi rakiyar gawar sa suka koma Wittenberg, a inda taron jama’a suka taru domin yi masa ban-kwana ta ƙarshe.
Dab kafin mutuwar sa, Luther ya yi wa’azi da ya kasance wa’azin sa na ƙarshe daga gadon sa na jinya a Eisleben. Wa’azin ya ƙunshi nassoshi biyu da ya ɗauko, ɗaya daga Zabura, ɗayan kuma daga Wasiƙun Bishara. Luther ya ambaci Zabura ta 68:19, “Albarka ga Ubangiji, wanda Yake ɗauke da nawayar mu kowace rana; Allah shi ne ceton mu. Luther ya sake ambaton Yahaya 3:16. Allahn mu zahiri Allah mai ceto ne, kuma wannan ceto ya samu ne ta wurin aikin Ɗan Sa.
Lucas Cranach, wanda mai zane ne, Ya yi wani zane na ƙarshe wa abokin sa, don tunawa da shi. An maƙala wannan zanen a kan bagadi a ikklisiyar Castle. Cikin zanen an nuna Luther yana wa’azi taron jama’a na ci-gaba da sauraro. Cranach ya haɗa da zana Katie matar Luther a cikin zanen. Haka ma ya saka ɗiyar Luther, Magdalena (wadda ta mutu tana shekara13), a cikin zanen. Ya zana Yesu a tsakanin Luther da taron jama’a. Luther ya yi wa’azin Kristi, da kuma giciye shi da aka yi. Kuma sa’adda taron jama’a suka ji wa’azin Luther, ba su ga Luther ba, a maimakon haka sai suka ga Kristi da giciye shi da aka yi. Wannan shi ne abin gado da Luther ya bari.
Kuma wannan abin gado ya yi gaba nesa, ya wuce zamanin Luther.
A 1940, W.H. Auden ya rubuta wata waƙa ta tunawa da Luther da irin gado da ya bari. Ya kira gajeriyar waƙar da “Luther,” Ya kammala waƙar da waɗannan baitoci:
Dukan ayuka, Da shahararrun mutane, Da al’ummomi duk miyagu ne.
Amma adali ta wurin bangaskiya zai rayu…” ya yi kuka cikin tsoro.
Sai maza da mata na duniyar nan
Waɗanda ba su damuwa ko su razana a rayuwar su ba,
Su ka yi murna.
An fara buga wannan tsararren rubutu ne a shafin ma’katar bishara ta Ligonier.


