‘Yancin Zaɓi: Me Wannan Ke Nufi?
01/12/2025
Tun da Allah Ne Mai Mulki, Ya ya Mutane suke da ‘Yanci?
04/12/2025
‘Yancin Zaɓi: Me Wannan Ke Nufi?
01/12/2025
Tun da Allah Ne Mai Mulki, Ya ya Mutane suke da ‘Yanci?
04/12/2025

Muhimmin Dalili da Ya Haifar da Barata

Ana yawan dunƙula koyaswa ta Masu-Gyara dangane da baratarwa cikin waɗannan kalamai ‘sola fide’ wanda ke nufin “ta wurin bangaskiya kaɗai.” Kalamai na ‘sola fide’ yana riƙe da koyaswar cewa, barata na samuwa ne ta wurin bangaskiya kaɗai.

Ikklisiyar Roman Katolika, a yadda tarihi ya nuna, ita ma ta koyar cewa barata na samuwa ne ta hanyar bangaskiya kaɗai. Suna cewa, bangaskiya ita ce matakin farko ga barata. Ita ce masoma da tushe na baratarwar mu. Roma ta nace ga muhimmancin bangaskiya domin baratarwa. Don haka, a fili Roma ta amince da ɓangaren ‘bangaskiya’. Abin da Roma ba ta amince ba shi ne ‘kaɗai,’ cewan, duk da yake bangaskiya shi ne matakin farko, da masoma, da tushe na barata, amma kasancewar ta kaɗai bai isa ya yi tasiri ga baratarwa ba. Dole ne a sami wani abu banda bangaskiya domin a tsarkake mu – wani yanayi na dole. Yanayin dole shi ne wani abu da dole ya kasance kafin wani tasiri ko sakamakon ya faru, amma kasancewarsa ba ya tabbatar da samun sakamakon.

Misali, cikin yanayin mai dacewa, abin da ake bukata domin wuta ta kama shi ne iska mai kyau. Amma kuma ba haka yake a gare mu ba, kasancewar iska mai kyau ba ta iya jawo wuta. Idan da haka ne ai da muna kama wuta da zarar mun shaƙi iska ta hancin mu. Don haka muna bambanta tsakanin yanayi da ake buƙata da kuma macancancin yanayi. macancancin yanayi yana ba da tabbaci zihiri cewa sakamakon da ake nema zai biyo baya. 

Bisa ga wannan kyakkyawan bayani, za mu gane bambanci tsakanin ra’ayin Roman Katolika da na Masu-Gyara game da dangantakar da ke tsakanin bangaskiya da barata. A ra’ayin Roman Katolika, imana yanayi ne da ake buƙata zuwa ga barata, amma ba macancancin yanayi ne ga samun barata ba. Amma a ra’ayin Wadanda-suka-Ware (Protestants), sun ce, bangaskiya ba kawai yanayi da ake buƙata kaɗai bane, amma har ya kasance macancancin yanayi ga barata. Ma’ana kenan, sa’adda muka sa bangaskiya da amincin mu cikin Kristi, zihiri Allah sai kira mu baratattu a gaban Sa. Ra’ayi na Masu-Gyara (Reformation), wanda shi ne tsari na Littafi Mai Tsarki, yana cewa, idan bangaskiya tana nan to, tabbas ne barata tana nan ita ma.

Abin da ra’ayin Masu-Gyara ke faɗa, wanda bai dace ba shi ne cewa, mutum zai iya samun bangaskiya ba tare da tsarkakewa ba. Ba za mu iya samun tsarkakewa ba tare da bangaskiya ba, kuma ba za mu iya samun bangaskiya ba tare da tsarkakewa ba. Roma tana cewa ba za mu iya samun tsarkakewa ba tare da bangaskiya ba, amma za iya samun bangaskiya ba tare da tsarkakewa ba. Za mu iya rike bangaskiyarmu amma mu aikata babban zunubi wanda zai lalata alherin tsarkakewa, har ya kai mu ga halaka (idan ba mu yi cikakkiyar tuba ba). Amma a wurin Masu -Gyara, mallakar bangaskiya ta gaskiya kadai it ace abin da ake bukata domin mu karbi alheri kuma mu ci gaba da kasancewa a matsayin wadanda aka tsarkake.

Ikrar ta ce:

Bangaskiya, wanda shi ne karɓan Kristi da hutawa cikin Sa, da adalcin Sa, shi ne kaɗai dalilin barata.  Ana amfani da wata na’ura, wato, kayan aiki wajen cimma burin wani takamammen abu muhimmi. A lokacin da masu tsara furucin bangaskiya na Westminister suka rubuta cewa, bangaskiya shi ne ne kaɗai dalili na barata, suna sane da jayyayyar nan da ke a ƙarni na goma sha shida a kan dalilin da ya haifar da barata. Yana da matukar muhimmanci a sami kyakkyawan fahimta na wannan koyarwa -dalili da ya haifar da barata -domin gaba ɗaya yana magana ne kan yadda aka cece mu. 

Wannan furuci na dalili (ko na’ura) da ta haifar, tana nan a tarihi tun ƙarni na huɗu kafin zuwan Kristi, ga mafalsafin nan Aristotle. Ya mai da hankalin wajen bayyana motsi da canji. Cikin wannan yanayi, ya yi ƙoƙarin ware irin dalilai daban-daban da kanjawo canzawar wani abu daga matsayi ko kamannin sa. Ta ya ya wannan ya shafi tambayar da muke yi a nan? Mu, a yanayin halittar mu, ba baratattu bane. Marasa adalci ne mu, kuma matsayin mu a gaban Allah shi ne cewa mun cancanci cikakken fushin Sa mai ƙuna marar yankewa. Muna buƙatar canji na matsayin mu, daga matsayi na waɗanda aka hukunta, zuwa matsayi na baratattu.

Aristotle ya fito da wasu muhimman abubuwa huɗu da kan zama musabbabin abu: Dalili na tsari, da dalili na inganci, dalili na ƙarshe, da dalili na kayan aiki. Bai haɗa da na dalili na musabbabi ba. Ko da yake waɗannan dalilai nasa guda huɗu sune tushen da ya kai ga tunanin dalili na musabbabi.

Ya bayyana wannan da misali na mutum-mutumi, wanda a farkon sa kasancewa dutse ne daga wurin tonon dutse. Aristotle ya bayyana babban dutsen a matsayi dalili na kayan aiki, wato, ainihin abu wanda daga jikin sa ne aka kirkiro wani abu daban. Tsararren dalili kuma shi ne, tunani da ya faru a zuciyar mai-kirkirar, ko kuma zubi da tsari na yadda yake son kammalallen aikin ya kasance. Dole ne akwai tunani a zuci kafin sakamakon ya zama zahiri a fili. Yanayin Inganci kuma shi ne, matakin da ke mayar da dutsen nan ya zama mutum-mutumi na dutse, kuma wannan masassakin dutsen kenan. Shi ne ya tabbatar da hakan ya faru. Sannan yanayi na dalilin ƙarshe shi ne ainihin maƙasudin yin wannan abun, wanda a nan zai iya zama domin kawai don a ƙara wa lambu kyau.

Ga duk dalilan nan huɗu za mu iya ƙara ainihin dalili na zahiri, wanda shi ne hanyar da canji ya sami yiwuwa. Idan masassakin yana so ya mai da babban dutsen ya zama mutum-mutumi, dole sai ya yi ta sassake dutsen nan har ya fito da zubi da siffar, kafin ya fara goggogewa ya bayyanu fyes. Gizagon sa da hamar sa su ne kayan aikin, wato, hanyar da canji ke samuwa. Mukan bayyana dalili da wasu kalamai cewa, ta kaza, ko kuma don kaza.

Sa’adda Masu-Gyara suka ce barata ta bangaskiya ne ko ta dalilin bangaskiya, suna nanata cewa hanyar ko kuma na’urar da ta ba mu barata ita ce bangaskiya kuma bangaskiya shi kaɗai. Abin da muke buɗata, ko kuma na’urar da muke buƙata domin mu tashi daga matsayi na la’ana zuwa matsayin barata shi ne bangaskiya, amma ba bangaskiya kaɗai muke buƙata domin samun barata ba. Gaba da wannan muna buƙatar Kristi don samun barata. Wato, domin mu kai ga samun barata muna buƙatar adalcin Sa da kaffarar Sa na giciyen. Shi ne dukkan abin da Allah ya buƙata domin kai wa ga adalcin Sa mai-cancanta, da hukuncin sa ya cika sosai da sosai na zahiri a cikin Kristi, da kuma ta wurin aikin Sa. Ya cika aikin duka. Gaba ɗaya dai muhawara game da barata wanda ke tsakanin Roman Katolika da Waɗanda-suka-Ware, ba takamaimai a kan aikin haƙiƙa da Kristi ya yi bane, amma ya fi mai da hankali kan yadda muka sami karɓan riban aikin Sa. Ya ya aka yi aikin Kristi na haƙiƙa zai sami daidaita ta wurin tunanin mutum? Amsar da Waɗanda-suka-Ware suka bayar, a bisa ga koyaswar Manzo Bulus ita ce, ‘ciki’ da ‘ta’ bangaskiya, ko kuma ‘dalilin’ da ‘ta wurin’, bangaskiya kaɗai.” Amma ba bangaskiya kaɗai ne ya cece mu ba. Idan muka ce barata ya zama ta bangaskiya kaɗai, kenan muna cewa barata ya yiwu ne ta bangaskiyar mu da kuma cikin bangaskiyar mu ga Kristi kaɗai.

A faɗin Roman dalilin da ya haifar da barata, shi ne, baftisma da nadama. Roman sun bayyana waɗannan ayukan ibada masu tsarki a matsayin hanyoyin da ta dalilin su da, kuma ta cikin su mutum yake samun barata. Bambanci ne a fili tsakanin ceto da aka samu ta hanyar aikata ayukan ibada masu tsarki (ta abubuwan tsarki da ikklisiya ta tsara) da kuma ceto da ake samu ta hanyar sa bangaskiya cikin Kristi kaɗai. Wannan shi ne muhimmin bambanci babba a duniya duka. Furucin ya bayyana cewa  bangaskiya shi ne kaɗai dalilin barata, domin ta wurin bangaskiya ne kaɗai muke da salama cikin Kristi, muke kuma karɓan adalcin Kristi. Adalcin Kristi, wanda muka amfana da shi dalilin kaffarar Sa, da cancanta na hakikanin, da dalilin barata, an ba da su ne kyauta ga duk wanda ya gaskanta. “Mai Adalci ta bangaskiya za ya rayu” (Romawa 1:17). ba mu sami tsarkakewa ta dalilin bangaskiya haɗe da ayuka ba, amma ta bangaskiya kaɗai. Duk abin da ake buƙata zuwa ga shiga mulkin Allah shi ne, bangaskiya ko gaskantawa ga aikin da Kristi ya yi kaɗai.

Bangaskiya ba shi ne dalilin baratarwar mu ba. Dalilin baratarwar mu ita ce adalcin Kristi, macancancin sakamakon Sa. Masu-Gyara sun ce macancancin sakamako da ya haifar da baratarwar mu shi ne adalcin Kristi kaɗai. Hanyar kai wa ga barata ita ce bangaskiya, amma idan muka ce mun sami barata ta bangaskiya kaɗai, ba wai muna cewa bangaskiya shi ne aiki macancanci wanda ya yi ƙarin wani abu akan dalilin baratarwar mu ba.

Ko wannan yana da wani tasiri a aiwace? Akwai mutane dayawa da ke cewa sun ba da gaskiya akan barata ta wurin bangaskiyar kaɗai, amma suna dogaro ga bangaskiyan kansu kamar shi ne ya zama abun da ya cancanta, ko ayuka na kirki da za su gamsar da abinda hukuncin Allah ke buƙata. Cewan mutum yana da bangaskiya, ba wai yana ƙara wani abin cancanta ga rayuwar sa a gaban Allah ba. Yana ƙara cancanta marar iyaka ga rayuwar sa, amma cancanta ta Kristi aka ba shi. Muna iya karɓan wannan cancantar Kristi ta hanyar bangaskiya ne kaɗai, wanda kuwa babu buƙatar wata cancanta don samun wannan. 

Wanda kaɗai zai iya ceton mu shi ne Kristi, kuma hanya kaɗai da za mu iya kai wa wurin Sa ita ce, ta bangaskiya. Ba ma dogaro ga wani abu a rayuwar mu sai Kristi kaɗai, da adalcin Sa domin ceton mu.

An tsakuro daga Ire-Iren Gaskiya Da Muke Furtawa na R.C. Sproul.


An fara buga wannan tsararren rubutu ne a shafin ma’katar bishara ta Ligonier.

R.C. Sproul
R.C. Sproul
Dr. R. C. Sproul shi ne ya kafa Ministirin Ligonier, shi ne kuma mai bishara da koyarwa na farko a masujadar Saint Andrew’s da ke a Sanford, Fla., Shugaba na farko na Reformation Bible College, kuma Babban darekta na mujallar Tabletalk. Har yau, ana yaɗa shirin sa na Renewing The mind (sabonta tunani) a dubban tashoshin radiyo a kewayen duniya, haka kuma ana iya sauraro a yanar gizo. Ya wallafa litattafai fiye da dubu, sun haɗa da, The Holiness of God (TSarkin Allah), Chosen by God (zaɓin Allah), da kuma Everyone’s a Theologian (Kowa Dalibin Tauhidi ne). Ya zama sananne a kewayen duniya domin kalaman sa na kishin kare Littafi Mai Tsarki a matsayin babu kuskure a ciki, da kuma buƙatar mutanen Allah su tsaya daram bisa amincin su a kan Kalmar Sa (Allah).