
Mene ne Ranar Gyara
06/01/2026
Abubuwa 5 da Ya Kamata Ku Sani Game da Zama Uba
13/01/2026Shawarar Luther Domin Rayuwa ta Krista
Dangane da yadda za a tafiyar da rayuwa ta Krista, mene ne nufin kasancewar Allah Mai-iko duka ne bisa kowa da komai, da ceto ta wurin alheri, da barata ta wurin gaskantawa, da sabon rai cikin zumunta da Kristi, yake nufi? Ga Luther, waɗannan batutuwa suna ɗauke da tasiri guda huɗu:
Tasiri na farko shi ne, fahimtar cewa, mai bi Krista ya kasance (simul iustus et peccator),1duk cikinlokaci guda wanda aka baratar duk a hakan kuma mai zunubi ne. Wannan tsari wanda mai yiwuwa rubutun John Tauler na Theologia Germanica ne ya zuga Luther, ya zama babban tsari da ya kawo daidaitawa: ga ni kaina, da kuma a ciki na, ina ganin mai zunubi ne ni kawai, amma idan na dubi kaina cikin Kristi, sai in ga mutum da aka lissafta a matsayin adali ɗauke da cikakkiyar adalcin Sa. Irin wannan mutum ya iya tsayawa a gaban Allah a matsayin adali kamar yadda Yesu Kristi ma yake -domin shi adali ne kaɗai ta dalilin adalci da ke na Kristi. A nan ne muke tsaye cikin tabbaci.
Tasiri na biyu shi ne, fahimtar cewa Allah ya zama Uban mu a cikin Kristi. An karɓe mu. Ɗaya daga cikin bayanai masu kyau da za a gani cikin rubutun Luther na Table Talk ya kasance, wata kila shi ne rubutun da John Schlaginhaufen, wanda ake ganin yana yawan kasancewa cikin baƙin ciki, amma kuma ake ƙaunar sa, ya taɓa rubutawa mai muhimmanci:
Tabbas Allah yana nuna min kyakkyawar abota, kuma yana magana da ni cikin hali mai kyau fiye da yadda Katty take magana da ɗan karamin Martin. Tsakanin Katty da ni babu wanin mu da zai ƙwaƙule idanu, ko ɓalle kan ɗan mu ko ‘yar mu. Haka nan Allah ma ba zai yi ba. Haƙiƙa Allah yana haƙuri da mu. Ya ba da shaidar hakan, domin haka ne ya aiko Ɗansa cikin jikin mu domin mu ƙwallafa begen mu a gare shi, don samun abu mafi kyau da mafi muhimmanci.2
Na uku, Luther ya nanata cewa, rayuwa cikin Kristi, lallai ta kasance rayuwa ƙarƙashin giciyen.3 Idan muna tarayya da Kristi, rayuwar mu za ta zama cikin tsarin da Nasa take. Hanyar da ke mafita ga ikklisiya ta gaske, da kuma Krista na gaske ba ta cikin tauhidin ɗaukaka (theologia gloriea), amma bisa ga tauhidin giciyen (theologia crucis). Wannan ya shafe mu matuƙa daga cikin mu, wato, ta yadda muke mutuwa ga ayuka na son ran mu, a bayyane kuma shi ne ta yadda muke tarayya cikin wahalar ikklisiya. Dole ne ta hanyar tauhidin giciyen a yi nasara bisa tauhidin ɗaukaka na tun lokacin ƙarni na tsakiya. Domin duk da banbancin ra’ayi game da fahimtar ainihin tsarin sakaramenti (sacraments)wadda Luther da Calvin suke da shi, sun sami yarda a wannan ɓangaren. Idan muna tarayya da Kristi cikin mutuwar Sa da tashin Sa, wanda aka alamta cikin baftisma ɗin mu (kamar yadda Bulus ya koyar a Romawa 6:1-14), to kenan rayuwa ta Krista gaba ɗaya za ta kasance ɗaukan-giciye:
Giciyen Kristi ba wai yana nufin wannan itacen da Kristi ya ɗauka a kafaɗar Sa wanda daga baya aka giciye shi a kai bane, amma gaba ɗaya yana nufin duk tsananin ƙunci na masu Bi waɗanda wahalar su wahalar Kristi ce, 2 Korintiyawa 1:5: “ … Azabai na Kristi suna yalwata zuwa gare mu”; haka kuma: “ Yanzu dai murna ni ke yi cikin azabai na sabili da ku, ina cika abin da ya gaza wajen ƙuncin Kristi cikin jiki na sabili da jikin Sa, wato, Ikklisiya kenan( Kolosiyawa 1:24). Giciyen Kristi gaba ɗaya yana nufin dukan tsananin ƙuncin ikklisiya wadda ta sha domin Kristi.4
Tarayya da mai-bi ke da ita tare da Kristi cikin mutuwar Sa da tashin Sa, da kuma yadda take aiwatuwa cikin yanayin rayuwar mu na kullayomi, a ra’ayin Luther, ya zama, madubin wanda Krista yakan koyi yadda zai dubi duk wani yanayi na rayuwa. Wannan -theologia crucis -shi ne ke kawo dukan abubuwa zuwa kyakkyawan fahimta, da kuma ba mu damar ainihin gane yanayin hawa da sauka na rayuwar Krista:
Sanin waɗannan abubuwa ya zama mana da riba, don kada baƙin ciki ya murkushe mu, ko kuma mu karaya sa’adda muka ga cewa magabtan mu suna matuƙar tsanantawa, da ware mu, suna kashe mu. Amma bari mu yi tunani tare da juna, bisa ga misali na Bulus cewa muna fahariya ne cikin giciyen, wanda muke ɗauke da shi, ba domin zunuban mu ba, amma domin Kristi. Idan muna tunanin cewa don kanmu ne kaɗai muke shan tsanani, za su kasance ba kawai da jin nauyi ba amma har ma ba za mu iya jure ɗauka ba; amma sa’adda muke iya cewa; “Wahalolin Ka (Ya Kristi) sun yawaita a cikin mu”; ko kuma kamar yadda yake a Zabura 44:22 “Saboda Kai ake kashe mu a kowane lokaci.” zai zama kuwa waɗannan wahaloli ba kawai suna da sauƙi ba, amma har ma suna da daɗi, dangane da waɗannan kalaman: “ Kaya na ba su da nauyi, kuma karkiyata mai-sauƙi ce” (Matiyu 11:30).5
Na huɗu, rayuwar Krista tana cike da tabbaci da kuma murna. Wannan shi ne ɗaya daga cikin ainihin muhimman alamu na Gyaran, lallai abu ne da ke a bayyane. Yadda Gyaran ya zo da kara samun fahimta game da barata -wato, a maimakon yin ayuka da begen kai wa ga barata, sai rayuwar Krista tana ainihin farawa da barata -wannan fahimta ta kawo kuɓuta na ƙwarai, yana cika tunani da ɓangaren ra’ayi, da muraɗin mu da murna sosai. Yana nufin cewa mutum zai iya fara rayuwa cikin hasken fahimta na rayuwar tabbas, ta nan gaba, kuma mai ɗaukaka. Babu wata gardama, wannan haske ya sake haskawa ya dawo cikin rayuwar yanzu, yana kawo matuƙar sauƙi da ‘yantarwa.
Tsayawa bisa kanka
A ra’ayin Luther, rayuwar Krista rayuwa ce da ta kafu-cikin-bishara, ta ginu-cikin-bishara, rayuwa ce mai kawo girmamawa-ga-bisharar da ke nuna ‘yanci da girman alherin Allah, kuma rayuwa ce da ake yi cikin matuƙar godiya ga Mai-ceto wanda ya mutu domin mu, muna tare da Shi cikin ɗaukan giciye har sai an haɗiye mutuwa cikin nasara, sannan bangaskiya ta fito a bayyane.
Mai yiwuwa, a shekara ta 1522, lokacin da suka zauna suna sauraron wa’azin Luther a wani ran Lahadi a ikklisiya da ke Borna, wasu daga cikin taron jama’a sun yi ta tunanin ko mene ke ƙunshe a tushen wannan bishara, wadda ta ainihin sa shi murna, har ma ta canza dan’uwa Martin. Ko tana yiwuwa su ma hakan ya faru da su? Luther ya iya fahimtar tunanin su. Ya hau bagadi a shirye domin ya amsa tambayoyin su.
Amma mene ne Bisharar? Ita ce wannan, cewa Allah ya aiko Ɗan Sa cikin duniya domin ya ceci masu zunubi, Yahaya 3:16, ya kuma murƙushe jihannama. Ya yi nasara kan mutuwa, ya ɗauke zunubi ya kuma gamsar da doka. Amma mene ne kuke da buƙatar yi? Babu komai, sai dai ku karɓi wannan, ku kuma kafa begen ku ga Mai-fansar ku da kuma ainihin yarda cewa ya aikata duka waɗannan abubuwa domin jin daɗin ku kuma ya ba ku su kyauta, a matsayin naku domin ko a cikin razanarwa ta mutuwa, da zunubi, da jahannama, zaku iya furtawa cikin tabbaci, mu kuma dogara a kai cikin ƙarfin zuciya, mu ce: Ko dayake ban iya cika doka ba, ko dayake zunubi na ciki na har yanzu, kuma ina tsoron mutuwa da jihannama, amma duk da haka, a cikin bishara na sani cewa Kristi ya ba ni dukan aikin da ya yi a kyauta. Na amince ba zai yi ƙarya ba, tabbas zai cika alƙawarin Sa. Kuma domin nuna alamar hakan ne na ɓarbi baftisma. A bisa wannan ne na kafa amincewa ta. Domin na sani cewa Ubangiji na Kristi, ya yi nasara kan mutuwa, da zunubi, da jihannama, da kuma shaiɗan domin jin daɗi na. Domin ya kasance marar laifi, kamar yadda Bitrus ya ce: “Shi wanda bai yi zunubi ba, ba a kuwa taɓa jin yaudara a bakin sa ba.” 1 Bitrus 2:22. Saboda haka zunubi da mutuwa ba su iya hallaka Shi ba, jihannama ba ta iya riƙe Shi ba, kuma ya zama Ubangijin su, ya tanadar da wannan ga duk waɗanda suka karɓa, suka kuma gaskanta da hakan. Duk wannan yana yiwuwa ne ba ta wani aikin kaina ko cancanta ba; amma ta alheri ne, da nagarta, da jinkai tsantsa.6
Luther ya taɓa cewa, “idan har na gaskanta cewa Allah ba ya fushi da ni, zan iya tsayawa a kan kaina don murna.”7 Mai yiwuwa a wannan ranar wasu daga cikin masu sauraron wa’azin sa, sun amsa kiran kuma sun ɗanɗana wannan “ƙarfin zuciya” da ya ke magana da ita. Wa zai iya sani ma ko wasu matasa, daga cikin mutane masu sauraron sa, sun rubuta suna bayyana wa abokan su cewa, sun je gida, sun tsaya bisa kawunan su don murna?
Sakon edita: An tsakuro wannan daga The Legacy of Luther sannan aka yi bugu na farko ran 29 na Oktoba 2018.
- Bayani mai maimaitawa a cikin Luther, misali, Luther: Lakcoci akan Romawa, 127, 208, 322. ↩︎
- LW, 54:127. ↩︎
- Don nassoshi da yawa game da wannan ƙa’ida a cikin Luther, duba Walther von Loewenich, Tauhidin Luther na Gicciye, trans. Herbert J.A. Bouman (Minneapolis: Augsburg, 1976), 112–43. ↩︎
- Luther, Sharhi akan Wasiƙar St Paul zuwa ga Galatiyawa, 558. ↩︎
- Ibid., 559. ↩︎
- Cikakken Wa’azin Martin Luther, 1.2, 373. ↩︎
- WA, 176.6f, wanda Oberman ya ambata, Luther: Mutum tsakanin Allah da Iblis, 315. ↩︎


