
Tun da Allah Ne Mai Mulki, Ya ya Mutane suke da ‘Yanci?
04/12/2025
Kafofin Da Aka Samo Asalin Tsarin Tauhidi
08/12/2025Ko Gyare-gyaren Sun Ƙare
Akwai abubuwa da dama waɗanda wasu da nake kira “Ibanjelikas (Evangelicals) a da” suka tanadar game da wannan batu. Ɗaya daga cikin su ya rubuta cewa, “Luther ya yi daidai a ƙarni na goma sha shida, amma zancen baratarwa ba wani babban abu bane yanzu.” Wani ma da ya bayyana kansa a matsayin Ibanjelika ya yi kalamai a wani taron manema labarai wanda ni ma na kasance, ya ce, “muhawarar nan na masu Gyara a ƙarni na goma sha shida game da Barata ta hanyar bangaskiya kaɗai, ya kasance “rikici kan abin da bai taka kara ya karya ba.” Bayan haka, wani su sanannen Masanin Tauhidi a turai ya yi gardama cikin rubutun sa cewa, koyawar barata ta hanyar bangaskiya kaɗai, a yanzu dai ba wani muhimmin abu bane a ikklisiya. Muna nan muna fuskantar mutane da dama waɗanda ake bayyana su a matsayin Furotestan (protestants) wato masu-bambamcin-ra’ayi, amma ya nuna a fili cewa sun manta kwata-kwata ko mene ne abin da suke bambancin ra’ayi a kai.
Idan muka lura da akasin waɗannan ra’ayoyi na zamanin yau, kan muhimmancin koyaswar barata ta hanyar bangaskiya kaɗai, za mu tuna wani ra’ayi na daban daga Mahukunta-masu-Gyara. Luther ya yi shahararren furucin nan nasa cewa koyaswar barata ta bangaskiya kaɗai ita ce abu wanda akan ta ne ikklisiya za ta iya tsayuwa ko faɗuwa. John Calvin ya ƙara nasa kwatance daban, ya ce barata ita ce madauri wanda komai yake juyawa a kansa. A ƙarni na ashirin, J.I. Packer ya yi amfani da kwantancin da ke nuna cewa, barata ta hanyar bangakiya kaɗai ita ce, kafaɗar da duk sauran koyaswa take tsaye a kai.” Daga baya Packer ya tashi daga wannan kwatanci mai ƙarfi, ya koma ga wani mara ƙarfi, yana cewa barata ta hanyar bangaskiya kaɗai shi ne “makasudi na bishara.”
Tambayar da dole mu fuskanta dangane da waɗannan tattaunawa ita ce, mene ne ya canza tun ƙarni na goma sha shida? To dai, akwai labari mai daɗi da kuma mara daɗi. Labari mai daɗi shi ne cewa, mutune sun zama wadanda ba su da tsattsauran ra’ayi kan abubuwan addini kuma suna jurewa game da saɓanin ra’ayi kan batutuwan tauhidi. Ba ma ganin ana ƙona mutane a kan itace, ko a gallaza masu azaba a dalilin bambancin koyaswa na batutuwan addini. Haka ma mun gani a shekarun baya cewa cin-jibi na Roman ya kafu matuƙa bisa wasu muhimman batutuwa na aƙidun Kristanci na zahiri, kamar Allahntakar Kristi, da musayar da Ya yi wajen kaffara, da Ya maye gurbin mu, da yadda Ruhu ya bishe marubuta Littafi Mai Tsarki, alhali kuwa kristoci Ma-su-bambancin-ra’ayi sun watsar da ainihin wannan tunani gaba-dayanta. Mun ga Roman ta yi tsayin daka kan batutuwan da suka shafi rayuwar yau da kullum, kamar su zubar da ciki, da kuma ra’ayi na kowane mutum doka-ne-wa-kansa. A ƙarni na goma sha tara a majalisar Vatican ta 1, Roman sun nuna Ma-su-bambancin-ra’ayi a matsayin “fanɗararru da masu kawo tsattsaguwa.” Cikin ƙarni na ashirin a Vatican II, an kira Ma-su-bambancin-ra’ayi da sunan “ ‘yan’uwa da suka ware.” Mun gani a fili irin tsarin bambanci na waɗannan majalisu biyu. Labari marar daɗi kuwa, shi ne cewa, koyaswa dayawa da ta keɓe Ma-su-bambancin-ra’ayi waɗanda ke riƙe da aƙidun Kristanci na tun farko, daga kuma Roman Katolika a ƙarnoni na baya can, yanzu ana kiran su tsauraran aƙidu tun a ƙarni na goma sha shida. An bayyana kusan dukan muhimman tsare-tsare na nazarin dokokin Mariya cikin shekaru 150 da suka wuce. Koyarwar rashin kuskuren Paparoma ne a duk lokacin da yake zaune a kan kujerar sarautar sa, ko dayake an fara aiwatar da haka tun da daɗewa kafin a ɗora shi bisa tsarin shari’a, amma daga baya a 1870 cikin majalisar Vatican, an kafa shi an mai da shi kamar Allah ne ya bayar (wanda kenan dole a amince da shi domin samun ceto). Mun kuma ga cewa a cikin shekarun baya, tarayyar Roman ta wallafa sabon littafin koyarwa Katolika, wanda ba tare da wata rudani ba ya sake tabbatar da koyarwar Majalisar Trent, ciki har ma’anar Trent game da koyarwar barata, (kuma saboda haka yana tabbatar da la’antar da wannan majalisa ta yi wa koyarwar Gyaran Addini (Reformation) cewa barata ta bangaskiya ne kadai). Haɗe da sake nanata abin da aka zartar a Trent, akwai sake nanata wasu koyaswar Roma game da fogatiri (purgatory) (wani wuri da in mutum ya mutu cikin zunubi zai je ya sha hukunci sannan daga baya ya shiga Sama), da hanyoyin samar da gamsuwa, da kuma baitul-mali na lada iri-iri.
A wata tattaunawa da shararrun masana tauhidi suka yi game da yadda koyaswar barata ta bangaskiya kaɗai ke ci-gaba da zama da muhimmanci, Michael Horton ya yi tambaya cewa, mene ne ya sa a cikin kusan shekaru goma da suka wuce, bisharar ƙarni na farko ta yi sanyi ta zama ba ta da muhimmanci kuma? Saɓani da ake da shi game da baratar ba akan ƙwarewa a sanin tauhidi bane, wanda aka keɓe daga waje-wajen ma’adana na gaskiyar Littafi Mai Tsarki. Ko kuma a gan shi kamar ba abun da ya taka kara ya karya bane. Wannan abu ne mai matukar muhimmanci da ya wuce a ɗauka a yanayin haka kawai ne ba. Tambaya mai cewa, “me nake buƙatar yi domin in sami ceto” ainihin tambaya ce mai matuƙar muhimmanci ga duk wani wanda fushin Allah ke ƙuna a kan sa.
Mafi muhimmanci ma gaba da wannan tambayar shi ne amsar ta, domin amsar ta shafi ainihin zuciya ta gaskiyar bisharar. A ƙarshen nazarin duka, Ikklisiyar Roman Katolika ta nanata a Trent, kuma har wa yau tana nanata cewa, abin da zai sa Allah ya kira mutum adali ko ba adali ba, wai yana samuwa ne cikin “hallayar adalci da aka halicci mutum da ita.” Idan har adalci ba ya cikin halayyar mutum, cewa in ta ɓace sai mutum ya shiga jahannama ko kuma in ta yi sauƙi (idan akwai sauran wasu abubuwa na rashin adalci cikin sa) sai mutum ya je wurin nan da zai sha tsanani na wani ɗan lokaci (Fogatiri) wanda zai iya kai wa tsawon miliyoyin shekaru. Bayyananne kuma zahirin akasin wannan, wato, ra’ayin Littafi Mai Tsarki da na Masu-bambancin-ra’ayi (Furotestan) game da hanyar samun barata, shi ne cewa, ainihin abin da ya ba mu barata shi ne adalcin Kristi, adalci wanda ake ɗora wa mai bi da ya yi imani, ta yadda da zarar mutum ya kasance da ainihin imani na ƙwarai da gaske, to duk abin da ake buƙata domin ceto, ya zama nasu ta dalilin ɗora masu adalcin Kristi. Muhimmmin batun na ainihi shi ne: wane dalili ne ya kai ga har na kasance da adalci na kaina? Ko kuma kamar yadda Luther ya faɗa, “wani baren adalci ne” wani adalci da ke a wajen mu, a ware daga mu -adalcin wani, wato, adalcin Kristi? Tun ƙarni na goma sha shida har zuwa yanzu, a kullum Roma ta ci-gaba da koyaswa cewan barata ya dogara ne ga imani ga Kristi da kuma alheri. Bambancin da ke tsakanin waɗannan matsayi biyu shi ne, irin yawan bambanci da ke tsakanin ceto da akasin ceto. Babu matsala mai tsananin girma da ta kai wannan a cikin rayuwar mutum wanda ke nesa da Allah mai adalci ya ke fuskanta.
A yanzu ikklisiyar Roman Katolika tana tir da da koyaswan nan na Littafi Mai Tsarki na samun barata ta yin imani kaɗai, ta musunta bishara, wanda ya sa ta daina zama ikklisiya ta gaskiya, duk kuwa da irin furuci da take yi na aƙidun Krista na ƙwarai na tun farko. Amincewa da ita a matsayin ikklisiya ta ƙwarai, bayan kuma tana ci-gaba da ƙin karɓan koyaswar Littafi Mai Tsarki kan ceto, ya kasance yanayi mai tsananin hatsari. Muna rayuwa a zamanin da ake ganin idan batutuwan tauhidi suna ƙin yarda da wasu matsayi na rayuwa, wai cewan wannan bai dace hakan ya kasance ba. Amma kuma idan ana ta cewa akwai salama bayan babu salama, ya zamana kenan cin amana ga zuciya da ran bisharar.
An fara buga wannan a mujallar Tabletalk.
An fara buga wannan tsararren rubutu ne a shafin ma’katar bishara ta Ligonier.


