
Muhimmin Dalili da Ya Haifar da Barata
02/12/2025
Ko Gyare-gyaren Sun Ƙare
05/12/2025Tun da Allah Ne Mai Mulki, Ya ya Mutane suke da ‘Yanci?
Allah ne mafi yanci, wato yancinsa ba shi da iyaka. Shi ne mai mafi Mulki duka. Yawanci, wurin da ake samun matsala kan kasancewar Sa Mai mulki, shi ne cewa, a zahiri in lalle Shi mai Mulki ne, to mutum ba zai iya zama mai yanci ba. Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da batun ‘yanci wajen bayyana wasu yanayi na ɗan Adam ta hanyoyi biyu da suka bambanta: ‘yanci daga taƙura, yanayin wanda mutum yake da damar yin zaɓi ba tare da taƙurawa ba, da kuma ‘yanci na tafiyar da ɗabi’a rayuwar nagarta, hali ne da muka rasa a lokacin da ɗan Adam ya faɗi, ya bar mu a matsayin bayi ga sha’awoyin jikin mu. Mabiya ra’ayi mai cewa, mutum shi ne doka da ƙa’ida wa kansa, sun yarda da cewa mutum zai iya yin zaɓi ba tare da taƙura ba, kuma cewa zai iya yin zaɓi ba tare da yiwuwar bijirewa da kansa zuwa ga aiwatar da abubuwa cikin mugunta ba. Dole ne mu Krista mu zama da tsaro, muna yin tsayayya da irin waɗannan ra’ayi na cewa mutum shi ne doka da ƙa’ida wa kansa, ko daga irin ra’ayin masu addinin gargajiya na ‘yancin ɗan Adam.
Ra’ayin Krista game da wannan shi ne, Allah ya halicci dukan mu ɗauke da halin daukar niyya, da kuma hali na iya yin zaɓi. Mu halitta ne masu dama na iya yin zaɓi. Amma kuwa wannan hakkin ‘yanci da aka bayar a lokacin halitta yana da iyaka. Muhimmin abu babba da ya ƙayyade ‘yancin mu Shi ne hakkin ‘yancin Allah. A nan ne muke faɗawa cikin matsalar saɓani tsakanin ikon Allah bisa kowa-da-komai, da kuma hakkin ‘yancin ɗan Adam. Wasu na cewa ikon Allah na mai mulki yana da iyaka saboda hakki na ‘yancin ɗan Adam. Idan kuwa haka ne, to kenan ɗan Adam shi ne Mai mulki ga kansa, ba Allah ba. Ra’ayin masu Gyara kan batun imani, ta koyar cewa hakkin ‘yancin ɗan Adam zahiri ne, amma girman Allah na Mai mulki ya iyakance shi. Ba za mu iya ɗora hakkin ‘yancin mu ya ture irin shirin Allah wanda ya kasance bisa kowa da komai ba. Domin hakkin ‘yanci na Allah yana da girma matuƙa, gagara misali ne.
Yanayin Tsarin zaman rayuwar iyali ya tanadar da misali. Iyaye suna nuna iko akan ɗa ko ‘ya.
Ɗan ko ‘yar na da ‘yanci amma hakkin ‘yancin iyaye ya fi girma. ‘Yancin da ɗa ko ‘ya ke da shi bai iyakance hakkin ‘yanci na iyayen ba, ba kamar yadda hakkin ‘yancin iyaye yakan ƙayyade na ɗa ko ’ya ba.
Idan muka zo ga halayyar Allah, dole ne mu fahimci cewa hakkin ‘yanci na Allah yana bisa dukan komai.
Idan muka ce Allah ne Mai mulki, muna bayyana wani abu game da hakkin ‘yancin Sa, ko dayake mukan yi tunanin cewa kasancewa Mai mulkiya bambanta da hakkin ‘yanci. Allah Mai iko duka ne bisa nufin Sa. Yana da nufin Sa, kuma yana ɗaukan matakai. Sa’adda yake shirya manufofin Sa, yana tabbatar da waɗannan shiri Nasa, Yana yin haka da cikakkiyar ikon Sa na Mai mulki gaba da dukan komai. Hakkin ‘Yancin Sa ‘’yanci ne da ya fi kowane iri. Shi kaɗai ne yake mai matuƙar iko kan komai duk a cikin Sa. Shi doka ne da iko gaba ɗaya, da kan Sa.
‘Yan Adam suna matuƙar son su kasance da irin wannan matsayi wa kan su da kansu, wato, hakkin ‘yanci marar iyaka, ba tare da muna ba da amsa ga wani ba, game da yadda muke tafiyar da rayuwar mu. A gaskiya ma, abin da ya faru kenan lokacin da mutum ya faɗi. Shaiɗan ya yaudari Adamu da Hauwa’u su nemi matuƙar hakkin ‘yancin kai, su zama kamar Allah, su aikata duk abin da suke so, ba tare da wani sakamako ya sauko masu ba.
Shaiɗan ya gabatar da tsari na gwagwarmayar neman ‘yancin kai a lambun Aidan, domin ya ‘yanta ‘yan Adam daga karɓan sakamakon laifi, da kuma ƙin kasancewa a ƙarƙashin shugabancin ikon Allah.
Allah ne kaɗai ne Mai dukan iko bisa kowa da komai gaba ɗaya.
An tsakuro daga Truths We Confess (Ire-iren Gaskiyar da muke furtawa) na R.C. Sproul.
An fara buga wannan tsararren rubutu ne a shafin ma’katar bishara ta Ligonier.


