
Shawarar Luther Domin Rayuwa ta Krista
08/01/2026
Abubuwa 5 da Ya Kamata Ku Sani Game da Aure
15/01/2026Abubuwa 5 da Ya Kamata Ku Sani Game da Zama Uba
Kwanan nan na zama kakan kakanni inda muka yimaraba da jikoki mata biyu da jikan namiji guda daya ɗaya cikin iyalinmu. Ga wasu ra’ayoyi na Littafi Mai Tsarki game da renon yara da nake bayarwa ga jikokina da matansu.
1. Kula da yara muhimmin kira ne da Allah ya ba ku.
Zabura ta 78 ta zo a zuciya:
Ya [Allah] kafa shaida a cikin Yakubu,
ya kuma kafa doka a Isra’ila,
wadda ya umarci kakanninmu
su koya wa ‘ya’yansu,
domin tsara mai zuwa ta san su,
‘ya’yan da ba a haifa ba tukuna,
su tashi su faɗa wa ‘ya’yansu,
domin su sa begensu ga Allah
, kada su manta da ayyukan Allah. ( Zabura 78:5–7)
Me zai fi muhimmanci fiye da bayar da gaskiya game da Allah ga tsara mai zuwa? Menene zai iya zama gado mafi muhimmanci fiye da tsara bayan tsara suna sanya begensu ga Allah? Za ku sami ƙalubale masu yawa a rayuwarku, amma kaɗan ne za su taɓa yin tasiri kamar renon yara “cikin horo da koyarwar Ubangiji” (Afisawa 6:3).
2. Koyon zama ƙarƙashin iko abu ne mai muhuminci.
Afisawa 6:1–3, Allah yana yi wa yara magana: “Ku ’ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku, gama ku na Ubangiji, abin da ya dace ku yi ke nan. Doka ta farko wadda aka haɗa da alkawari ita ce, “Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, don ka zauna lafiya, ka kuma yi tsawon rai a duniya.” Allah ya zana da’ira wadda yara za su rayu a cikinta. Iyakar da’irar ita ce a girmama iyaye da kuma yin biyayya ga iyaye. Allah ya yi alƙawarin albarkatu masu ban mamaki yayin da yaro ke zaune a cikin da’ira; zai yi kyau, kuma za su ji daɗin tsawon rai
Waɗannan albarku ne da kowane yaro da iyaye ke so. Girmamawa da biyayya ya fi zurfi fiye da kawai yin abin da aka gaya wa mutum. Imani ne na amincewa da kuma yi wa Allah biyayya. Yayin da kake koya wa yaranka su kasance ƙarƙashin iko, kana nuna anihin gaskiya cewa biyayya ga ikon Allah ita ce hanyar samun albarka.
3. Zuciya ita ce tushen rayuwa.
Ka kiyaye zuciyarka da dukkan tsaro,
domin daga gare ta ne maɓuɓɓugan rai ke fitowa. (Karin Magana 4:23)
Rayuwa tana gudana daga zuciya. Matsalar da muke da ita ba wai kawai ta ƙunshi hanyoyin da muke yin zunubi ba ne, har ma da zunubin da ke ƙarƙashin zunubi. Girman kai, son kai, hassada, da halaye daban-daban na zunubi na zuciya ne ke motsa hali. Yana da sauƙi ga iyaye su mai da hankali kan hali su kuma kasa lura da zuciya.
Yesu ya tunasheu cewa halaye kamar kwadayi, yaudara, hassada, zagi da irman kai, kuna fitowa daga zuciya (duba Markus 7:2-23). Babban ɓangare na aikin iyaye shine taimaka wa yara su gano halayen zuciya da ke ƙarƙashin hanyoyin da suke yin zunubi. Tabbas, fahimtar halayen zuciya da ke ƙarƙashin zunubanku masu wahala zai sauƙaƙa yin tambayoyi masu kyau waɗanda ke taimaka wa yaranku su fahimci zukatansu.
4. Ka sanya bishara ta zama tsakiyar komai.
Zuciyar bangaskiyarmu ba ita ce yadda za mu zama masu nagarta don samun rai madawwami ba. Zuciyar bangaskiyarmu ita ce Wanda ya isa. Yesu ya zama jiki domin ya zama Mai Cetonmu. Ya yi rayuwar da ba za mu iya rayuwa ba; Ya rayu ba tare da zunubi ba domin mu sami adalci. Ya mutu mutuwar da ba za mu iya mutuwa ba; Ya ba da ransa a kan giciye domin ya cece mu daga laifi da hukunci na zunubanmu. An tashe shi zuwa rai domin mu sami ceto. Har ma yanzu yana yi mana addu’a a hannun dama na Uba.
Wannan begen alheri, gafara, ceto, da ƙarfafawa gaskiya ce da ‘ya’yanmu (da mu kanmu) ke buƙata koyaushe. Yayin da kuke gyara kuma kuke almajirtar da su, koyaushe kuna riƙe begen bishara a gaban ‘ya’yanku. Muna musanta bishara lokacin da muka gaya wa yara cewa za su iya zama nagari da ƙarfinsu. Ƙarfafawar Ibraniyawa 2:17 ita ce Yesu wanda, a matsayinsa na mutum, ya sha wahala da jaraba, zai iya taimaka mana a cikin jarabobinmu.
5. Abin da ka nuna ta hnayar halayenka yana da karfi sosai.
Kubawar Shari’a 6:5 ta ɗauke wannan gaskiyar: “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan ƙarfinka.” Ƙaunarka ga Allah, farin cikinka a cikinsa, da godiyarka da gamsuwarka ga duk abin da Allah yake a gare ka cikin Almasihu gaskiya ne masu mahimmanci da yayanka za su iya yin koyi da su. Ayoyi na gaba sun nuna muhimmancin wannan koyi: “Waɗannan kalmomi da na umarce ka a yau za su kasance a zuciyarka. Za ka koya wa ‘ya’yanka su da himma” (Kubawar Shari’a 6:6–7).
Kowace rana, yayin da kake zaune tare da ‘ya’yanka, kana gabatar da ra’ayi na gaskiya. Kana nuna musu cewa ka yi imani cewa Allah nagari ne kuma mai bada lada ga waɗanda ke nemansa. Ta hanyar ƙaunar Allah da mutane, kana kwaikwayon gaskiya cewa dokar Allah tana da kyau. Yayin da kake fifita ibada, kana gaya musu cewa rayuwa tana cikin Allah. Idan kana kyautata wa mutanen da ba su da kirki, kana nuna girman Allah da alherinsa. Duk abin da kake yi yana ba wa ‘ya’yanka labarin gaskiya.
Sadaukarwarka ga Allah a cikin komai, gaskiyarka game da yadda zuciyarka ke yawo, da kuma begenka ga alherin bishara duk suna ba wa ‘ya’yanka labari. Renon yara don Allah yana ɗaya daga cikin manyan ayyukan da za ka taɓa yi.
An fara buga wannan labarin a shafin yanar gizo na Ligonier Ministries.


