
Me Muke Nufi da Girman Kirista?
17/11/2026Ikon Tsarkin Allah da ke Canza Rayuwar Yau da Kullum
Makonni bayan juyowa ta ga Kristi, yawancin abokaina suna da tambayoyi a gare ni, musamman game da abin da wannan yake nufi ga al’amuran shakatawar dare na a nan gaba: Shin zan ci gaba da fita? Shin an “yarda” mini in sha giya? Tambaya ɗaya da ta yi fice a waɗancan kwanaki na farko ta fito ne daga mahaifin abokina. Ya tunkare ni ya tambaya, “Yaya abin yake sanin cewa ga sauran rayuwarka, kowa zai kasance a waje yana jin daɗi da walwala yayin da kai kuma ka maƙale wajen zuwa ikilisiya?” In na waiwaya baya yanzu, nakan yi murmushi game da irin wannan tambayar, amma a lokacin ta sa ni tambayar kaina a hankali: Shin a shirye nake (kuma zan iya) in bar irin rayuwar shagali da nake yi”? Shin a shirye nake in kasance a ikilisiya ranar Lahadi? Shin, in yi amfani da kalmomin Manzo Bulus, a shirye nake in manta abubuwan da suka wuce, in fuskanci abin da ke gaba da ƙwazo? (Filib. 3:13).
Irin wadannan tattaunawa sun faru akai-akai a cikin shekaru na fiye da talatin na bin Kristi, kuma abin da aka fi mayar da hankali a kai a duk lokacin da aka fuskanci irin waɗannan tambayoyi kullum ya kasance na duniya ne. Kullum game da ni ne da sha’awoyina, wane ne ni, da kuma abin da nake so. Bai taɓa zama game da Allah da sha’awoyinsa ba, wane ne Shi, da kuma abin da Yake so. Wannan ba abin mamaki ba ne; bai kamata mu taɓa tsammanin wanda ba mai bi ba zai yi tunanin abin da ya wuce na zahiri ba. Waɗannan abubuwa waɗanda suke haɗe da Kristi ne kawai za su iya fahimtarsu. Kamar yadda Bulus ya ce, “Mutum na ɗabi’a ba ya karɓar al’amuran Ruhu na Allah, gama wauta ne a gare shi, kuma ba shi da ikon fahimtarsu domin ta hanyar ganewar ruhaniya ake gane su” (1 Kor. 2:14).
Wannan ya kai ni ga batun wannan rubutu: Ikon Tsarkin Allah da ke Canza Rayuwar Mutum. Watanni bayan na zama Kirista, ya bayyana a gare ni cewa muradina na barin al’amuran wannan duniya a baya, kuma a maimakon haka in bi tsarki, ya dogara ne a kan sanin da na samu ta wurin shaida game da Allah cikin Almasihu. Gwargwadon yadda fahimtata game da ko wane ne Allah ta yi zurfi, haka ma ƙwadayina na in zama kamarsa yake ƙaruwa. Wannan gaskiya ne musamman idan ya zo ga batun tsarkin Allah.
Tsarkin Allah ba halaye ce kawai daga cikin halayensa ba,—shi ne tushe kasancewars da kuma ainihin abin da Shi yake. Shi ne cikakken tsarkinsa, kammalar ɗabi’a, da kuma rabuwa gaba ɗaya daga duk abin da yake na yau da kullum ko mara tsarki. Kamar yadda masanin tauhidi Louis Berkhof ya faɗa, Allah mai tsarki “ya bambanta da dukan halittunsa, kuma ya ɗaukaka sama da su cikin girma marar iyaka.”1 Tsarki shi ne halin Allah kadai da aka nanata da maimaitawa sau uku, “Mai tsarki, mai tsarki, mai tsarki” (Isha. 6:3; Ruy. 4:8). Wannan sanarwa ta tsarki sau uku tana jaddada cewa Allah keɓaɓbe ne sarai—babu wani kamarsa. Joel Beeke ya bayyana wannan kamar haka: “An keɓe shi ta wurin ɗaukakarsa, domin ɗaukakarsa. . . . Shi mai tsarki ne saboda wanda shi yake a matsayin Allah, [kuma Shi] mai tsarki ne domin ya himmatu sosai wajen nuna wanda shi yake a cikin duk abin da yake yi.”2
Ba kamar tsarkinmu ba, wanda yake da aibi kuma marar daidaito, tsarkin Allah madawwami ne kuma marar canzawa. Yana bayyana komai da Allah yake yi. Alal misali, ƙaunar Allah mai tsarki ce; adalcinsa mai tsarki ne; jinƙansa mai tsarki ne; ikonsa mai tsarki ne; gaskiyarsa mai tsarki ce. Don haka, fahimta da rungumar tsarkin Allah zai canza yadda muke tunani, rayuwa, da kuma yin bauta.
Sa’ad da muka haɗu da tsarkakar Allah da gaske, ana canza mu. Yi la’akari da Ishaya 6. Ishaya ya ruɗe da ganin bayyanar tsarkakar Allah. Ya ruɗe baki ɗaya, yana kuka, “Kaito na!” (Ish. 6:5). Haɗuwa da tsarkakar Allah yana ƙanƙantar da mu, yana bayyana zunubinmu, kuma yana sake fasalin tunaninmu da zukatanmu, yana tilasta mana mu daidaita muradinmu da nufinmu da nasa muradin da nufinsa. Kuma muradin Allah da nufinsa a gare mu shi ne mu zama masu tsarki domin Shi mai tsarki ne: “Ku zama masu tsarki, domin ni mai tsarki ne” (Lev. 11:44; 1 Bitrus 1:16). Da yake mun gane bukatar da muke da ita gare shi, an ware mu domin nufinsa kuma an canza mu zuwa kamaninsa.
Bayyana wannan filla-filla ya wuce ƙa’idar wannan ɗan gajeren tunani, amma darasin mai sauƙi ne: Idan kuna son ku zama kamar Kristi, ku yi kowane ƙoƙari don ku san Allah Mai Tsarki—Uba, Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki. Ku karanta littafin R.C. Sproul mai suna The Holiness of God, ko na J.I. Packer mai suna Knowing God, ko kuma na Stephen Charnock mai suna The Existence and Attributes of God. Mafi mahimmanci, ku karanta Nassosi cikin addu’a da nufin haɓaka iliminku game da Kristi. Kamar yadda D.A. Carson ya faɗa:
Mutane ba sa neman yin rayuwa mai tsarki da kansu. Sai dai idan alherin Allah yana taimaka mana mu yi kokari, ba za mu dage wajen rayuwar tsoron Allah, yin addu’a, yin biyayya ga Littafi Mai Tsarki, da kuma farin ciki cikin Ubangiji ba. Maimakon haka, muna iya karkata zuwa yin abin da bai dace ba…. har ma mu fara yarda da wasu abubuwan da ba su da tushe.3
Sanin Allah Mai Tsarki sosai, da kuma sanin Almasihu, yana taimaka mana mu daina bin wannan hanyar da ba ta dace ba, ya sa mu bi hanyar tsarki, kuma ya ba mu tabbacin rayuwar da za ta kasance cike da farin ciki da jin dadi na har abada. Saboda haka, lokaci na gaba da wani ya tambaye ka, “Yaya yake sanin cewa har tsawon rayuwarka, kowa zai fita yana nishaɗi da jin daɗin rayuwa yayin da kai kuma dole ya sa ka zuwa ikilisiya?” yi murmushi ka ce: “Da a ce ka san Allahna mai tsarki, da a ce ka san Yesu, ba za ka yi wannan tambayar ba. Zuwa ikilisiya don bauta masa shi ne abin farin cikina, gama shi kaɗai ne zai iya cika zuciyata da murna da kuma yalwar farin ciki!” (Zab. 16:11; Isha. 35:10; Yoh. 16:24).
1. D.A. Carson, Domin Ƙaunar Allah: Abokin yau da kullum don Gano Wadatar Maganar Allah, Littafi na 2 (Good News Publishers, 2006), kamar yadda aka nakalto a Goodreads.com. ↩
2. Louis Berkhof, Summary of Christian Doctrine (Banner of Truth, 2011), 28. ↩
3. Joel R. Beeke da Paul M. Smalley, Reformed Systematic Theology, Vol. 1 (Crossway, 2004), 569. ↩
An wallafa wannan makala ne da fari a Ministirin Ligonier Blog. [Blog ɗin Ministirin Ligonier]


