Ta Yaya Zan Iya Yin Magana da Hikima?

10/11/2026

Me Muke Nufi da Girman Kirista?

17/11/2026

Ta Yaya Zan Iya Yin Magana da Hikima?

10/11/2026

Me Muke Nufi da Girman Kirista?

17/11/2026

Biye da Kalubalen Zama Uwa da Alheri

Wannan lokacin bazara yana kawo babban sauyi a matsayina na uwa: auta na zai kammala karatun sakandare. Wannan ita ce ƙarshen wannan mataki na renon yara. Na daɗe ina hango hakan kuma ina cike da tarin motsin rai daban-daban—farin ciki ga ɗana yayin da yake shiga mataki na gaba na rayuwa; baƙin ciki yayin da nake tsammanin rashin ganinsa a gida kowace rana. Na isa makasudin da dukanmu muke tafiya zuwa gare shi, duk da haka ina cike da rashin tabbas game da abin da ke nan gaba.

Lokacin da na fara wannan tafiya, na ji nauyin dukan abubuwan da ban sani ba ya mamaye ni. Na ji ba ni da cancanta a gaban abubuwa da dama da suke sababbi kuma ba a san su ba. Na rasa hikima don yanke shawara masu wuya na rainon yara kuma na ji tsoron kada in kasa yin su daidai. Tun daga wannan lokacin, na fuskanci yanayi masu wahala da yawa a zamana na uwa kuma ina sa ran wasu za su zo. Duk da haka, zan iya duban baya in ga alherin Allah yana aiki da kuma amincinsa na tallafa mini a cikin dukan wahalhaluna.

Duk inda kike a tafiyarki ta zama uwa—ko a farkon shekaru, ko tsakiya, ko kuma lokacin da yara suka bar gida—Allah yana saduwa da ke a inda kike. Yana tanadar da alherinsa. Muna ganin wannan a rayuwar wasu iyaye mata uku a cikin Littafi Mai Tsarki. A kowane yanayinsu, Allah ya tanadar da abin da suke bukata kuma ya ba su alherinsa.

Allah Yana Gani kuma Ya Sani

A cikin labarin Hajaratu, muna ganin wata wadda take dab da zama uwa wadda Allah ya gani a cikin gwagwarmayarta. A matsayinta na bawanatatar Sarai, ta zama sashe na shirin Sarai na sa alkawuran Allah su tabbata (Far. 16). Lokacin da ta gudu daga fushin Sarai zuwa cikin jeji, Allah ya sadu da ita kuma ya nuna mata alherinsa. A can ta kira Allah El Roi; “Kai Allah ne mai gani . . . Lalle a nan na ga wanda yake lura da ni” (Far. 16:13). Lokacin da daga baya ta sake samun kanta a hamada kuma ta yi tunanin ita da ɗanta za su mutu, Allah ya gan ta. Ya ji kukan ta. Ya sake biya mata buƙatunta da alherinsa: “Kada ki ji tsoro, gama Allah ya ji” (Far. 21:17).

Sa’ad da muke fama a matsayinmu na uwaye, Allah yana saduwa da mu a inda muke da yalwar alherinsa. Shi ne El Roi, Allah mai gani. Yana ganin tsoronmu, baƙin cikinmu, da rashin tabbas ɗinmu. Ya san damuwarmu game da yaranmu. Yana jin kukanmu na neman taimako kuma yana ceton mu. Mafi girman shaidar wannan ita ce ceton da Allah ya yi mana daga zunubanmu a kan gicciye, inda ya bayar da nasa Ɗan don ya biya hukuncin da ya kamata a yi mana. Ta wurin ba da gaskiya ga aikin Kristi a madadinmu, an cece mu daga zunubi kuma yanzu mu na Allah ne: “Idan Allah yana tare da mu, wane ne zai yi gaba da mu? Shi da bai rage wa kansa nasa Ɗan ba, amma ya ba da shi saboda mu duka, ta yaya ba zai kuma ba mu dukan abu kyauta tare da shi ba?” (Rom. 8:31–32).

Allah ɗaya wanda ya ga Hajaratu cikin jeji yana gani kuma yana jin kukanmu na neman taimako.

Allah Yana Ceto Saboda Ƙaunar Alkawarinsa

A cikin littafin Rut, mun haɗu da Na’omi, wadda ta rasa kome a ƙasar Mowab. Mijinta ya mutu, sannan ‘ya’yanta maza biyu su ma suka mutu. Baƙin cikinta ya yi nauyi; ba ta iya tunanin cewa rayuwa za ta sake kawo mata farin ciki ba. Allah ya yi mata tanadi ta wurin surukarta Rut, wadda ta bar mutanenta domin ta bi Na’omi a tafiyarta ta komawa gida zuwa Baitalami. Bayan haka, Ya yi mata tanadi a cikin gonakin hatsi na miji mai ƙauna ga Rut da kuma jika ga Na’omi. Wani jigo da yake yawan fitowa a cikin labarinsu shi ne Kaunar Allah mai suna “hesed.” Irin wannan ƙauna ta fi alheri kawai; ita ce sadaukarwar alkawari na Allah ga mutanensa.

Allah yana saduwa da uwaye a cikin mawuyacin hali da ƙaunarsa ta hesed. Ga iyaye mata a cikin yanayi mai wuya, ga waɗanda ke cikin mawuyacin lokaci na raino, za mu iya dogara ga amintacciyar ƙaunar Allah gare mu. Ƙaunar da take da aminci. Ƙaunar da ke cetawa kuma take tanada. Ƙaunar da ke kiyaye alkawuranta. Ƙaunar da ba ta taɓa gazawa ba.

Allah nan guda ɗaya wanda ya ceci Naomi a cikin baƙincikinta kuma ya nuna ƙaunar hesed gare ta da kuma Rut, mai aminci ne a cikin ƙaunarsa gare mu.

Allah Yana Shirya Mu Domin Kiranmu

Wata rana matashiyar budurwa Maryamu ta haɗu da mala’ika Jibrilu, wanda ya gaya mata cewa za ta haifi Mai Ceton duniya. Na tuna sarai irin rashin iyawa da na ji sa’ad da nake sabuwar uwa; ba zan iya tunanin yadda abin ya kasance ga Maryamu ba sa’ad da ta ji irin wannan labari. Waƙarta tana tunatar da mu yadda Allah yake aiki a cikin rayuwarmu ta wurin alherinsa:

Gama shi wanda yake Mai Iko ya yi mini manyan abubuwa,
kuma sunansa mai tsarki ne.
Kuma jin ƙansa yana ga waɗanda ke tsoronsa
daga tsara zuwa tsara” (Luka 1:49–50).

Allah ba ya kiranmu a matsayin iyaye mata domin mun riga mun san abin da muke yi ba. Ba ya zaɓar mu mu yi rainon yaran da ya amintar mana don mu kula da su domin mu masu iyawa ne ko kuma masu hikima. Maimakon haka, yana tanadar mana dukan abin da muke buƙata na zama uwa daga cikin alherinsa mai yawa: “Gama ikon Allahnsa ya ba mu duk abubuwan da suka shafi rai da ibada, ta wurin sanin wanda ya kira mu zuwa ga tasa ɗaukaka da nagarta” (2 Bitrus 1:3). Yana ba mu dukan abin da muke buƙata don mu yi rainon yaranmu. Yana samar da hikima, ƙarfi, da jimiri. Wannan bishara ce ga iyaye mata.

Allah ɗaya da ya zuba alherinsa a kan Maryamu yana zuba wannan alheri a kanmu mu ma.

Kowace daga cikin waɗannan uwaye a cikin Nassi sun fuskanci alherin Allah a rayuwarsu, wanda ya bayyana amincinsa. Iyaye mata, ko a wane hali kuke a yau, ku amince cewa Allah zai same ku a can, ya kuma ba ku alherinsa.


An wallafa wannan makala ne da fari a Ministirin Ligonier Blog. [Blog ɗin Ministirin Ligonier]

Christina Fox

Christina Fox

Christina Fox tana aiki ne a sashen dangantaka da tsofaffin ɗalibai a Kwalajin Covenant a Lookout Mountain, Ga. Marubuciyar littattafai da dama ce, har da Closer Than a Sister. Ita mamba ce a East Cobb PCA a Marietta, Ga.