Akidar Manzani
Ina ba da gaskiya ga Allah Uba Mai iko duka. Mai halittar sama da kasa;
Ina ba da gaskiya ga Yesu Kristi Dansa Makadaici Ubangijimmu;
Wanda aka habila ta wurin Ruhu Mai tsarki,
Haifuwa tasa daga budurwa Maryamu;
Ya sha wahala cikin zamanin Bilatus Babunte;
Aka giciye shi, ya mutu, Aka bizne shi;
Ya tafi Hades.
Rana ta uku ya tashi kuma daga matatu;
Ya hau bisa cikin sama;
Yana zaune ga hannun dama na Allah Uba Mai iko duka;
Daga can za shi zuwa garin ya yi shari’a bisa masu rai da matatu.
Ina ba da gaskiya ga Ruhu Mai tsarki;
Ekklesiya mai tsarki Katolika; Zumuntar Tsarkaka;
Gafarar zunubai;
Tashin jiki; Da rai mara matuka. Amin.