Kalmar da aka mayar jiki
Furucin Ligonier kan akidar Kristi

Muna furta asiri da al’ajibi
na Allah da aka mayar jiki
kuma muna murna cikin ceton mu mai girma
ta wurin Yesu Kristi Ubangijin mu.

Tare da Uba da Ruhu Mai Tsarki,
Ɗan ya halicci dukan komai
Yana riƙe dukan abubuwa,
da kuma sabonta dukan abubuwa,
Zahiri Allah,
Ya zama zahiri mutum,
Kasancewa biyu cikin ɗaya.

Shi wanda Budurwa Maryamu ta haifa
Ya yi rayuwa a cikin mu.
Aka giciye shi, Ya mutu, aka binne Shi,
Ya tashi a rana ta uku,
Ya hau zuwa Sama,
kuma zai sake dawowa
cikin ɗaukaka da hukunci kuma.

Domin mu,
Ya kiyaye doka,
Ya yi kaffara don zunubi,
ya kuma gamsar da fushin Allah mai ƙunna
Ya ɗauki ƙyallayen mu masu ƙazanta,
Ya ba mu,
Rigar Sa ta adalci.

Shi ne Annabin mu, da Firist, da Sarkin mu,
Yana gina ikklisiyar Sa,
Yana roƙo sabo da mu,
Yana kuma mulki bisa dukan abubuwa.
Yesu Kristi Shi ne Ubangiji;
muna yabon Sunan Sa mai tsarki har abada.

Amin.