Bayanin Imaninmu 

Ministrin Ligonier suna manne da tsoffin maganganun bangaskiya (Akidar Manzanni, Akidar Nicene, da Akidar Chalcedon) kuma suna tabbatar da bangaskiyar Kirista mai tarihi kamar yadda aka bayyana a cikin solas biyar na gyare-gyare da kuma yarjejeniyar ta ikirari ta gyare-gyare na tarihi (Ma’auni na Westminster, Forms of Unity, da 168th Baptisti na London).

Littafi Mai Tsarki

Littafi Mai-Tsarki, gabaɗayansa, Maganar Allah ce marar kuskure, kuma hurarra; wahayi ne na Ubangiji wanda yake dauke da cikakken nauyin ikon Allah kuma ya wajaba mu mika wuya gare shi.

Triniti

A cikin Ubangiji akwai haɗin kan wadannan ukun mabambanta, Allah Uba, Allah Ɗa, da Allah Ruhu Mai Tsarki; waɗannan ukun a zahiri ɗaya ne, Allah madawwami, iri ɗaya ne a zahiri, daidai suke cikin iko da ɗaukaka.

Allah

Allah Ruhu ne, marar iyaka, madawwami, kuma marar canzawa a cikin sa, cikin hikima, iko, tsarki, adalci, nagarta, da gaskiya. Allah mai cikakken sani ne, mai iko akan komai, kuma mai iko ne a ko’ina, ba ya koyo kuma “a sane yake da komai”

Yesu Kristi

Yesu Almasihu shi Allah ne cikakke Kuma mutum ne cikakke wannan yanayi biyu da ba sa rabuwa da juna cikin  allahntaka sa ba tare da ruɗani, gauraya, rabuwa, ko rarrabuwa ba. Kowane yanayi yana riƙe da halayensa. A cikin jiki, an haifi Yesu daga Budurwa Maryamu, ya yi rayuwa cikakka a cikinmu, an gicciye shi, ya mutu, an binne shi, ya tashi a rana ta uku, ya hau sama, zai dawo kuma cikin daukaka da hukunci. Shi ne kadai matsakanci tsakanin Allah da mutum.

Ruhu Mai Tsarki

Ruhu Mai Tsarki ɗaya yake da Uban da Ɗan. Ya wanzu har abada cikin Uban da Ɗan, kuma yana zaune a cikin zukatan masu bi, yana aiwatar da sabuntawar su ta hanyar cetonsu zuwa ga Ubangiji kaɗai, yana kuma aikin tsarkakesu a lokaci daya.

Halitta

Allah, ta wurin ikon kalmarsa ya halicci sammai da ƙasai da abin da ke cikinsu daga babu. Ya cigaba da kula da tafiyarda dukkan halittunsa da dukkan ayyukansu bisa ga mafificin tsarki, hikima da iko.

Mutum

Bayan da Allah ya halicci sauran halittu, ya halicci mutum namiji da mace cikin kamaninsa, amma saboda Adamu ya yi zunubi kuma ya fadi cikin hakkinsa, shi da zuriyarsa suka shiga halin ɓatanci na ɗabi’a da rashin ɗabi’a kuma suka rabu da Mahaliccinsu, don haka sun cancanci mutuwa a matsayin hukuncin zunubi.

Kafara

Domin kowa ya yi zunubi, dole ne a yi kafara domin mutum ya sulhunta da Allah. Yesu Kiristi ya yi cikakkiyar kafara domin mutanensa ta wurin maye gurbinsu da mutuwarsa akan gicciye. Ya lissafta adalcinsa ga dukan masu bi yana ba da cikakkiyar fansa ga duk waɗanda suka tuba daga zunubi kuma suka dogara gare shi kaɗai don ceto.

Dokar

Doka ta jiki tana nuna cikar halin Allah marar canzawa kuma har abada ta halarta akan dukkan mutane, masu bi da marasabi.

Ekkilisiya

Kristi ya kafa ikkilisiya da ake iya gani, wadda aka kira ta don ta rayu cikin ikon Ruhu Mai Tsarki a ƙarƙashin ƙa’idar ikon Littafi Mai Tsarki, wa’azin bisharar Almasihu, tafiya cikin tsarki,  da kuma horo.

Kiristanci da Al’adu

Ligonier suna goyan bayan ayyukan ƙungiyoyin Kirista da cibiyoyi waɗanda suka amince da ikon Nassin Yesu Almasihu a matsayin doka na karshe, da shugabancin Yesu Almasihu, kuma sun himmatu wajen aiwatar da abubuwan zamantakewa da al’adu na dokokin Allah don kyautata rayuwar mutum da muhallinsa. Ligonier musamman tana goyan bayan ƙungiyoyin da ke yin Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa ’yan Adam wadanda basu iya  yi wa kansu kariya a matakan girmansu,kuma suna ƙin chanza ma’anar jinsi, jima’i, da aure dake a Littafi Mai Tsarki.

Duba kuma Bayanin Ligonier akan Kiristi.