
Dalilin Da Ya Sa Gyarar Ke Da Muhimmanci Har A Yau
30/12/2025
Mene ne Ranar Gyara
06/01/2026Aƙidu da Furucin Imani na Furotestan
Al’amarin Gyara wani yunƙuri ne a kan muhimman batutuwan bangaskiya. Farkon farawa da Luther, sa’annan kuma da sauran al’adun Furotestan, masu-Gyara sun ƙayyade bangaskiyar Littafi Mai Tsarki bisa koyarwar Roman Katolika da kuma ikon paparoma. Nuni da Littafi Mai Tsarki a matsayin shi ne kaɗai tushen koyarwa, dole kuma sai da Furotestan suka sake bayyana fahimtarsu ta koyarwar Littafi Mai Tsarki. A wannan fannin, furucin Gyara sun zama abin ƙayatarwa na miƙa kan Furotestan ga Littafi Mai Tsarki.
Ba Furotestan ne suka kawo buƙatar furuci ba. Cikin ƙarnoni, ikkilisiya takan yi furucin bangaskiya cikin yanayin ruɗani ko rikici. Aikin aƙidar ko furucin ba domin ya ɗauki gurbin Nassi ba ne, sai dai don a taƙaita shaidar ikkilisiya ta gaskiyar da ke cikin Nassi a haskaka ta bisa kuskure.
Batutuwan da aka fi sani cikin misalan wannan aniyar su ne aƙidun tarihi –kamar aƙidun Nicene da na Chalkidoniya – waɗanda an rubuta tsakanin ƙarni na uku da na biyar. Waɗannan aƙidu sun samo asali ne daga irin buƙatun nan daga baya, kamar na furucin Furotestan – wato, buƙatar bayyana abin da ikkilisiya take ɗauka a matsayin muhimmin a kan batutuwan koyarwa.
Amma, abin da ya bambanta furucin Furotestan shi ne marmari a ɓangaren masu-Gyara domin yin gyara daga tushe har rassa. Batutuwan Gyara ba kawai gardama ba ne game da wata koyarwa guda – ko wasu jerin koyarwa ba – amma ya danganta ne bisa ga buƙatar gyara ikkilisiya a dukaninta. Wasu koyarwar, kamar Ɗaya Cikin Uku, an riƙe su a matsayin sun kafu bisa Littafi Mai Tsarki, sannan wasu, kamar baratarwa ta bangaskiya kaɗai, an buƙaci nazarinta sosai. Domin, ikkilisiyoyi a cikin al’adunsu, shugabannin Furotestan sun yi ƙoƙarin rubutu cikin sauƙaƙan kalamai kan tunanin da ya shafi karɓar koyarwar, kamar baratarwa ta bangaskiya kaɗai ko kuma ƙin koyarwar paparoma.
Wato, a wannan fannin, Furcin Furotestan iri ɗaya ne da aƙidun farko, sai dai sun fi bayyanuwa a zurfinsu. Kamar dai aƙida, ba su maye gurbin Nassi ba, kuma ba a dora su dadai a matsayinsa ba. Maimakon haka, furucin ne ke bayyana abin da Furotestan suka samu a cikin Nassi.
FURUCIN LUTHERAN
Misalin farko na wannan rukunin a aƙidar Furotestan ana samunsa a kwanakin farko na Gyaran Luther. Bayan gwagwarmaya domin baratarwa ta hanyar bangaskiya kaɗai a shekarar 1517 zuwa 1519, kuma bayan an kira shi mai laifi da mai ridda a majalisar Diet of Worms (1521), Luther ya yi aiki nan da nan don bayyanawa a rubuce maƙasudin saƙon sa cikin jerin takardun furuce-furuce. Guda biyu dai don ikkilisiya ne, ɗayan kuma don kariyar saƙon Luther ne a gaban jama’a.
A batutuwa biyu na farko, Luther ya rubuta Manya da Ƙananan Katkizin (Catechism, wato, addu’o’i na jagora)a shekarar 1529, na farko domin horon almajirai manya da fastoci, na biyun kuma domin yara da sabobbin tuba. Ya kuma rubuta jawabi don tuba (wato, Exhortation to Confession) a wannan shekarar domin nanata buƙatar furta laifofi. Duk da cewa Luther ya jadda da cewa ikkilsiya ta dogara bisa Nassi kaɗai, buƙatar tuba ta jama’a gaba ɗaya tana da muhimminci.
Waɗannan katkizim ɗin (littattafan addu’o’i) na farko suna kuma nuna alamar ɗaya cikin muhimman halaye na furta zunubai ko tuba: kayan aiki ne na almajiranci, masu muhimmancin gaske ga rayuwar ikkilisiya.
Furuci na uku shi ne sanannen furuci na Augsburg Confession (1530), wanda Luther da Philip Melanchthon suka rubuta, ba don tuba ta jama’a domin ikkilisiya ba, amma domin a bayyana ta a gaban Sarki Charles na Biyar da kuma yariman nahiyar Turai. Rubutu ne mai nanata saƙon Lutheran, mai tsauri a lafazi, ko kuma a yadda ake aikata ta. Yana bayyana abin da Lutherawa suka yi imani da shi ainihi bisa tuhumar da aka yi masu ta hannun Jamusawa ‘yan Katolika.
Wato kenan, addu’ar katkizim da furucin Lutheran yana cikin muhimman bayanai na hanyoyi da ake morar furta laifofi a zamanin Gyara: ɗaya domin rayuwar ikkilisiya, ɗayan kuma domin rashin jituwar jama’a a kan tuhume-tuhumen ƙarya game da aƙidar ƙwarai ta Furotestan; ɗaya domin kowane mai bi a cikin ikkilisiya, ɗayan kuma domin shugabannin ta su fayyace abin da suka riƙe a matsayin aƙidar koyarwa ta ƙwarai.
FURUCI DA AKA GYARA SUNA HABAKA
Al’adar Gyara tana kuma himmatuwa ga aikin furuci. Bisa ga faɗin abin da muka tattara, an samu kusan furuce-furucen Gyara kusan arba’in zuwa hamsin waɗanda aka rubuta tsakanin shekarun 1520 da 1650—wanda, nesa ba kusa ba, mafi yawa a kowace al’ada ta Furotestan. A shekarar 1523, kusan dab lokacin da al’adar Gyara ta fara, Huldrych Zwingli ya bayyana batutuwa Sittin da Bakwai (wato, Sixty-Seven Articles), domin ya tanada bayanin batutuwan da ke ci a Zurich. An bi bayan wannan da rubutun Ten Theses of Berne (1528), da furucin First Confession of Basel (1534), da kuma da yawan wasu birane suka fara rungumar ra’ayin Gyara. Wasu sun biyo baya a wasu ƙasashe, tare da na Faransa, da aka sami furucin French Confession of Faith (1559) da kuma ƙasar Scotland inda aka sami furucin Scots Confession (1560).
Dalilin furuce-furucen imani na Gyaran da yawa, yana zuwa ne saboda tsarinsu. A koyaushe, bangaskiyar Gyara tana zuwa ta jagorancin wata ƙungiyar ‘yan’uwa (duk da alamun zamani da ke nuna kamar cewa John Calvin ne kaɗai ya samar da aƙidar Gyara). Amma an haifar da al’adar Gyara a birane dayawa da ƙasashe dayawa kusan a lokaci ɗaya. Daga shekarar 1520 zuwa gaba, birni bayan birni sun rungumi Gyara, sau ɗaya cikin ɗan lokaci, wasu lokuta kuma tun kamin gyaran ta iso Geneva. Don haka, babu wata murya ɗaya tak kamar ta Luther da ta tsara takardar furucin Gyara.
Sanadiyar wannan, ikkilisiya bayan ikkilisiya, al’umma bayan al’umma, sun nuna ƙuzari sosai wajen tsara furucin bisa yanayin ikkilisiyoyinsu. Wannan ne dalilin da ya sa mafi yawan furuce-furucen Gyara suke shaida kansu dangane da birninsu na asali: wannan ne furucin wannan birnin, ko wannan ikkilisiyar, ba wai don dukkan ikkilisiyoyin Gyara su rungume ta tamkar sifa ɗaya ga kowa ba.
Bugu da kari, kamar yadda masana tarihi da malaman tauhidi suka nuna, akwai tarayya na waɗannan furuce-furucen Gyara da suka haɗa waɗannan muryoyi daban-daban zuwa muryar Gyara ɗaya. Bambance-bambancensu ba dayawa ba ne har da za mu ga rarrabuwarsu a kan batutuwan ceto, ibada, da aiki. A yau, ikkilisiyoyi dayawa sun amince da muhimmin tarayya kan abin da ake kira Hanyoyi Uku na Ɗayantaka (Three Forms of Unity)—furucin Belgic Confession, furucin Canons na Dort, da kuma addu’ar Heidelberg Catechism—kasancewa ɗaya ba ta ikon ƙirƙirowa ba, amma shaida ta ƙa’idojin Gyara.
Wannan yana nufin cewa, dukkan furucin Gyara suna da kama. Yayinda bangaskiyar Gyara take yaɗuwa daga yankunan Swiss zuwa Jamus, Faransa, Netherlands, sa’annan zuwa Ingila da Scotland, an sami wasu bambance-bambance kan abin da ake jaddadwa da kuma yadda ake aiki da su. Waɗannan shaidu na furci su ne suka haɗa matakin farko da ya kawo bambance-bambance ga dariku da al’ummomin Gyara kamar yadda muka sani a yau.
MASU BIJIREWA A MAJALISAR DORT
A ƙasar Netherlands, ana misali, tasowar ra’ayin Arminianism a cikin ikkilisiyoyin Gyara sun tanadar da bayanin (yanayi na Synod of Dort (1618–19), yanayi na musamman na yadda ake morar ƙa’idar Gyara kan ƙalubalen Jacob Arminius. Dayake ya yi karatu a Geneva a ƙarƙashin magajin Calvin, Theodore Beza, Arminius ya koma don aiki a matsayin fasto. (Wani babban akasi ɗaya shi ne, Beza ya rubuta wasiƙar yabo don Arminius sa’adda ya koma gida.) Amma, Arminius ya yi ta samun shaka ame da sha’ainin ilimin Gyara da kuma koyarwarta a kan ƙaddara da alheri. A zamaninsa, koyarwarsa ta zama cibiyar koke-koke na wasu shugabanni dayawa, game da ra’ayin Calvinist.
Bayan mutuwar Arminius a shekarar 1609, matsayar Arminian—wadda aka kuma sani da bangaskiyar Remonstrant (Remonstrant faith) —ba da jimawa ba ta fito da abubuwa biyar da aka aika wa shugabannin yakin Dutch War don samun rabuwa daga yankunan Katolika da ke ƙarƙashin ikon Spain a Netherlands. Majalisar Dort ta yi zama saboda wannan, kuma ta ƙi dukan bayanai biyar ɗin da aka jero. Haka nan aka haifar da bayanai biyar da aka sani na Calvinism, duk da cewa manufar Majalisar Dort ɗin ba don ta rage bangaskiya zuwa bayanai biyar ba ne, amma dai don samar da amasoshi ga bayanai biyar da ra’ayin ( na Arminianism).
Ci-gaba zuwa ƙarshen ƙarni na goma sha bakwai, za mu ga irin wannan bayani na ƙa’idar Gyara a furucin London Baptist Confession of Faith (1689). Yayin haifar da aƙidar Furitan (Puritan) ta Baptist—ko tushen asali na Primitive Baptists—masu ra’ayin Calvinist ‘yan Dutch su ne suka rubuta wannan furuci na Gyara, waɗanda sun bambanta da Presbyterians, da Anglicans, da kuma Dutch Calvinists a fannonin siyasar su da kuma ƙin ra’ayin baftisma ga yara (paedobaptism). Wannan furucin ya zamanto adadin tsararraki na ‘yan Baptists da ya samo asali a Ingila, wanda ya zama muhimmi wajen bayyana ra’ayoyin Gyara na Baptist cikin ƙarnoni da suka bi baya.
TSARIN WESTMINSTER
Babban alama na furucin imani, shi ne Tsarin nan na Westminster, wanda ya ƙunshi furucin amincin bangaskiya, Dogo da Gajeren Katkizim (Catechism)wato, littafi da ya ƙunshi tsarin sujada na jama’a), da kuma tsarin da ya kamata ƙa’idar shugabancin ya kasance. Furucin amincin ya zama nuni ga Gyara na dokokin addini, sannan sauran Katkizim biyun sun kwaikwayi niyyar Luther na tanadar da littafin jagora wa fastoci da manyan mutane (Dogon Katkizim kenan), wa yara kuma (Gajeren Katkizim). Dangane da tsawo da faɗi kuma, babu wani tsarin furucin imani na lokacin Gyara, ko bayan lokacin Gyara da ya iya kai wa irin na Taron Westminster. Ko dayake tarihin su tana da tushe daga gwagwarmaya game da Furitanizim (puritanism) (ra’ayin tsarkake ikklisiyar Ingila (England) daga duk abubuwan da suka kasance al’adun Katolika).
Tun zamanin Henry na VIII (1509-47) ikklisiyar Ingila ta rungumi wani muhimmin ɓangaren furucin imani ne -Rubuce-rubuce Arba’in da Biyu na farko (a 1552) daga baya aka harhaɗa su suka koma Talati da Tara (a 1563). Ko dayake waɗannan rubuce-rubuce suna da tsarin Furotestan, ba su bayyana dalla-dalla yadda ikklisiya za ta aminci da ƙa’idojin sujada ba, kuma ba su ɗauki wani tsayayyen matsayi ba game da koyarwa da ke kawo saɓani, kamar su, tauhidi na tsarin shugabancin ikklisiya, da kuma cewa Yesu yakan kasance a lokacin cin jibi. Rashin yiwuwar rubuta kyakkyawan tsari na furucin imani da aka samu ba wai ta dalilin jan jiki bane, sai dai domin rashin dama da aka samu saboda munanan rashin yarda kan batutuwa tsakanin masu biyayya ga Furotestan da waɗanda ke biyayya ga katolika, wanda ya faru a ƙarƙashin ‘ya’yan Henry biyu, Edward VI da Mary I. A mafi yawan lokaci cikin ƙarni na goma sha shida, Ikklisiyar Angilikan (Anglican) ba ta sami gatar rubuta dogon furucin imani da ke haɗe guri ɗaya ba.
Zuwa lokacin Elizabeth ta I, dayawa a Ingila sun amince da wannan gajeren furucin imani a matsayin abu nagari. Gajerun Furucin imanin suna iya rage yawan tarkacen koyarwa da ke tasowa, misali tsakanin shugabanni Furotestan da na Ludaran (Lutheran) a Turai. Duk da cewan Bishop irin su Matthew Parker ya goyi bayan hasken bangaskiya da Gyaran ya kawo, amma kuma ya fara nuna damuwa game da yadda kiraye-kiraye suka yi yawa na cewa ikklisiyar Ingila ta canza matsayinta dangane da yadda za a aiwatar da ibada ko sujada, da yanayin sanya tufafi na fastoci da mawaƙa, da kuma game da irin koyarwa, da dai sauran hidimomi da suka shafi lokacin sujada.
Sakamakon wannan rashin amincewa ne ya haifar da tsarin Furitan, da farko a ƙarƙashin Elizabeth sannan zuwa lokacin James I ya ƙaru, masu wannan ra’ayi sun so ne a sake ci gaba da Gyaran, maimakon a sami yin bayanin dalla-dalla na abin da Furitan ɗin ya ƙunsa. Duk da haka, duk Furitan sun kasance da taƙaici kamar dai sauran mutane, game da jinkirin da su Bishop da ‘Yan siyasa suka nuna wajen ci-gaba da gyara Ikklisiyar Ingila.
Zuwa lokacin Charles I, yanayin ya ƙara yin duhuncewa. Ƙarƙashin shugabancin Elizabeth da James, yanayin da Furitan suka shiga shi ne an yin banza da su, ko dayake ba yi yawan tsananta masu ba, ko dayake Charles ya kasance da tsanin ra’ayi mummuna wa Furitan. A karshe, wannan rikici tsakanin majalisa da sarki ya kai ga Yakin basasa na Ingila (1642-51).
Furitan sun yi nasarar gwagwarmayar, ta aikin jarunta da Oliver Cromwell -wanda har yau, gunkin mutum-mutumi da aka yi nasa yana nan a gaban ginin majalisa. A lokacin yakin, majalisar ta umurta shugabanni na Furitan (da wasu mashawarta ‘yan kasar Scotland) su hada wani taro domin sake fadada wadannan Rubuce-rubuce Talatin da Tara su zama cikakkan furucin imani wanda zai yi daidai da wasu sauran furucin imani na Turai. Taron Westminster nan sun yi kokarin su cikin gaskiya don kafa aikin su bisa wadannan Rubuce-rubuce talatin da tara, amma ba da dadewa ba sun gane cewa wannan tsarin yana kuntatawa, saboda haka sai suka sake farawa daga farko.
Yanayin gwagwarmayar tawaye ga Charles, da kuma bukatar kara yin wasu Gyara, ya bayyana fadi da zurfi tsare-tsaren Westminster. Maimakon a ga tsarin a matsayin kokarin takaita dukan koyarwar, sai a ga tsarin a matsayin fashewa na tarin tunani da aka danne ne cikin su Furitan, tunani na yi wa Gyararrun koyarwa na Ingilishi, da ayukan da suke yi. An riga zub da jini, an bebentar da muryoyin, yanzu kuma da muryoyin suka sami ‘yanci daga wurin da aka tsare su, sun ga cewa nauyi ne ya rataya a wuyan su su bunkasa ba kawai game da ra’ayin su game da koyarwar abubuwan addini kadai ba amma har game da sujada da almajirantarwa, da wasu tarin muhimman batutuwa a rayuwar ikklisiya.
FURUCIN IMANI A YAU
A rayuwar ikklisiyoyin Furotestan a yau, ana amfani da furucin imani ta hanyoyi da dama. Ba duka abubuwan da zamani ya kawo ne Ikklisiyar ta Ibanjelikal (Evangelicals) ta karba da amince da su don ya zama furucin imani ba. Batutuwa masu karfi, irin su, tasowar Fetizim (pietism), da kuma gagarumin sake farfadowa na biyu (Second Great Awakening) ya jawo yanayi na sanyayawa ga matsayin furucin imani -na cikin taron jama’a ko in mutum na shi kadai sai suka daukaka furucin imani da sa a shirya nan take. Wani lokaci ana ganin furucin imani a matsayin yana toshe hanya ga imani na zahiri.
A sa’adda wadannan abubuwa da zamani ke kawowa suke zama abin ban tsoro, furucin imani na karni na shida da na bakwai ba su shude ba. Ana amfani da su kowane mako a ikklisiyoyi, ko a yanayi na lokacin sujada ko kuma idan ana yi wa sabobbin tuba da yara katkizim. Haka ma ana morar su wajen tabbatar da aminci da da’ar fastoci da dattawa a dariku dayawa. A ta wannan fuskar, furucin imani bai kasance shinge mai kayyadewa wajen tabbatar da bin koyarwar da zahiri kadai ba, amma har ana amfani da su a matsayi takardu na rayuwa da suke yin jagora ga almajirai Krista domin rayuwar yau da kullum.
An fara buga wannan tsararren rubutu ne a shafin ma’katar bishara ta Ligonier.


